in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron dandalin tattalin arziki na Davos
2014-01-23 14:48:09 cri

A ranar Laraba ne aka bude taron shekara-shekara na dandalin tattalin arziki na duniya a garin Davos na kasar Switzerland, inda sama da shugabannin siyasa da na tattalin arziki 2,500 daga sama da kasashe da yankuna 100 ke halarta.

Bayanai na nuna cewa, ya zuwa yanzu shugabannin kasashe da gwamnatoci sama da 40 sun isa garin na Davos don halartar dandalin na wannan shekara da aka riga aka bude a ranar Laraba.

Taken taron na wannan shekara wanda za a gudanar daga ranar 22 zuwa 25 ga wata shi ne, sake fasalin harkokin duniya, sakamakon da zai kasance ga al'umma, harkokin siyasa da cinikayya, inda ake sa ran tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arzkin duniya, kasuwannin masu tasowa, gyare-gyare kan harkokin kudi da matsalar canjin yanayi.

Kakakin taron, Schwab, ya ce, manufar taron ita ce, gano hanyoyin magance muhimman batutuwa, da nazarin makomarmu ta hanyoyin da suka dace. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China