in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya kara hasashen da ya yi kan karuwar tattalin arzikin duniya
2014-01-22 10:58:26 cri

Asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya dan kara hasashen da ya yi game da karuwar ci gaban tattalin arzikin duniya da kashi 3.7 cikin 100 a shekarar 2014, wato sama da kashi 0.1 cikin 100 kan hasashen da ya yi na watan Oktoba.

Asusun ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da rahotansa game da hasashen tattalin arzikin duniya, inda ya ce, tattalin arzikin duniya zai kara bunkasa a shekara 2014-15, musamman kan yadda tattalin arzikin kasashe masu karfin tattalin arziki zai farfado.

An kuma yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa da kasashe masu tasowa zai bunkasa daga kashi 4.7 cikin 100 a shekara ta 2013 zuwa kashi 5.1 cikin 100 a shekara ta 2014.

An kuma yi hasashen cewa, tattalin arzikin Sin zan dan yi kasa kadan daga kashi 7.7 cikin dari a shekara ta 2013 zuwa kashi 7.5 cikin 100 a shekara ta 2014.

Sai dai a watanni 6 na karshen shekarar 2013, tattalin arzikin kasar Sin ya kara farfadowa, sakamakon karuwar zuba jari da aka samu. Ko da yake masana na cewa, wannan na dan karamin lokaci ne, saboda manufofin da kasar ta aiwatar na hana karuwar bashi da gundarin uwar kudi. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China