Da yake tsokaci bayan kammala taron hadin gwiwar bankin duniya, da bankin bada lamuni na IMF a jiya Asabar, ministan kudin kasar Singapore Tharman Shanmugaratnam, ya ce yayin da tattalin arzikin duniya ke farfadowa, tattare da ragowar kalubale masu alaka, kamata yayi a maida hankali ga tsara matakan da zasu karfafa tattalin arzikin kasashe bisa matsakaitan zango a maimakon na gajeren zango.
Mr. Shanmugaratnam wanda kuma ke jagorantar kwamitin tsara manufofin asusun IMF, ya kara da cewa daukar wannan mataki ne zai bada damar samun daidaito, da ci gaban da ake fata a wannan fanni.
A cewar sa ministocin kudi, da jami'an manyan bankuna mahalarta taron na yini biyu, sun maida hankali matuka, wajen tattauna batutuwan da suka jibanci gudanar da sauye-sauye, ga manyan manufofin tattalin arzikin duniya. (Saminu Alhassan)