Wannan ziyarar ita ce ta farko da wani Shugaban kasar Sin ya kai Jamus a cikin shekaru 8. A lokacin ziyarar, Shugabannin kasashen biyu za su fitar da tsarin da dangantakar kasashensu za ta bi nan da shekaru 5 zuwa 10 da zai kawo dabarun ci gaba da hangen nesa.
Lokacin da ya isa Berlin, Shugaban Xi ya ce, hadin gwiwa tsakanin Sin da Jamus ta samu nasarorin masu dimbin yawa tun lokacin da kasashen biyu suka kulla huldar diplomasiyya shekaru 40 da suka gabata, sannan kuma kasashen 2 na da ra'ayi daya a kan fadada dangantakarsu da bullo da sabbin hanyoyin hadin gwiwa.
A cikin jawabinsa, Shugaba Xi ya ce, yana sa ido wajen yin aiki da shugabannin Jamus domin su bullo da hanyoyin inganta ci gaba tsakanin kasashen biyu ganin cewa, an tuntubi mutane daga bangarori daban daban na kasar Jamus a kan hadin gwiwa da kulla abota da kuma daukaka dabarun ci gaba na kasashen biyu zuwa wani sabon mataki.(Fatimah)