in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An watsa bayanin da shugaban kasar Sin ya rubuta a jaridar Faransa
2014-03-26 11:30:50 cri
Wata jaridar kasar Faransa mai suna Le Figaro, ta watsa jawabin da Shugaban kasar Sin mista Xi Jinping ya rubuta, mai taken 'abokan musamman da kawayen dake kokarin amfanar da juna'.

Jawabin da jaridar ta fitar a ranar 25 ga wata, jawabi ne na musamman da shugaban kasar ta Sin ya fitar domin wannan jarida ta kasar Faransa a wani bagare na ziyarar aikin da yake yi a kasar.

Cikin bayanin na sa, shugaba Xi ya jaddada cewa, kokarin kyautata huldar dake tsakanin Sin da Faransa da kasashen 2 suka rika yi shekaru 50 da suka wuce, ya sa an samu fasahohi, da kwarewa wajen kiyaye wannan abokantaka ta musamman, da ci gaba da kokarin amfanar bangarorin 2.

A cewar shugaban, kasashen Sin da Faransa na da nauyin kiyaye zaman lafiya a duniya, da neman samar da ci gaba na bai daya, kasancewarsu zaunannun mambobin kwamitin sulhun MDD. Shugaba Xi na ganin cewa kasashen 2, na da damar gabatar da nagartattun shawarwari, don tabbatar da kasancewar bangarori daban daban a duniya, da kokarin daidaita al'amuran duniya ta hanyar sulhu, gami da tinkarar kalubalolin da ake fuskanta, kamarsu ta'addanci, da sauyawar yanayin duniya.

A ci gaba da bayaninsa, Xi ya ce kasar Sin ta shiga wani sabon mataki na kokarin zurfafa gyare-gyare, da kara bude kofa ga kasashen waje, yayin da kasar Faransa ita ma ke kokarin gyarambawul ga tsare-tsarenta, don tabbatar da habakar tattalin arziki, da kara samar da guraben aikin yi, ta yadda za ta iya takara da sauran kasashen dake saurin bunkasuwa.

A ganin shugaban, matukar bangarorin 2 suna darajanta damar da suka samu a kokarin marawa juna baya, tabbas za a iya habaka huldar hadin gwiwa dake tsakanin su, kana za a iya kara kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2 a shekaru 50 masu zuwa. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China