A yau Alhamis 27 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda ke ziyara a kasar Faransa ya gana da Jean Marc Ayrault, firaministan kasar Faransa, inda Mr. Xi ya nuna cewa, kasashen Sin da Faransa sun fitar da shirin bunkasa dangantakar dake tsakaninsu irin na matsakaita da dogon lokaci, wannan zai taimakawa wajen bunkasa harkokin cinikayya a tsakaninsu da zuba jari ga juna. Ya kuma yi fatan bangaren Faransa zai samar da yanayin zuba jari mafi kyau ga kamfanonin kasar Sin, har ma kasashen biyu za su iya kara yin hadin gwiwa da sauran kasashe tare.
A nasa bangaren, Mr. Ayrault ya bayyana cewa, bangaren Faransa yana hangen nesa game da huldar dake tsakaninsa da kasar Sin daga dukkan fannoni, kuma yana son ci gaba da yin tattaunawa kan harkokin siyasa da sauran batutuwa iri daban daban. (Sanusi Chen)