Yayin ganawarsu, Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin tana yaba wa matukar a kan ayyukan hukumar UNESCO dangane da raya al'adu na daban daban. Ya ce abin a yaba ne musammam ganin yadda take mai da hankali kan aikin ba da ilmi ga jama'ar kasa da kasa, da ma yadda ta mai da ayyukan da ya shafi daidaiton jinsi da kuma Afirka a matsayi mafi muhimmanci, wanda hakan ya sa ta samu sakamako mai gamsarwa.
Shugaban Xi ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin kara yawan mutanen da take baiwa guraben karatu a kasashe masu tasowa ta hukumar UNESCO daga guda 25 zuwa 75, don goyon bayan kasashen Afirka wajen raya ayyukan ba da ilmi.
A nata bangaren kuma, Irina Bokova ta nuna godiya ga kasar Sin dangane da goyon baya da kasar ta baiwa hukumarta, ta yi imani cewa, ziyarar shugaba Xi a hukumar za ta ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu gaba. (Maryam)