A shekarun baya, gwamnatocin kasashen biyu sun yi hadin kai yadda ya kamata, matakin da ya baiwa kasashen biyu taimako wajen inganta dangantakar dake tsakaninsu. Ban da haka kuma, kasashen biyu suna kara hadin gwiwa kan wasu manyan batutuwan kasa da kasa, ciki had da kiyaye zaman lafiyar duniya, tsaron shiyya-shiyya, tinkarar sauyin yanayi, samun isasshen abinci, sa kaimi ga samun bunkasuwa mai dorewa da sauransu.
Dadin dadawa, babban burin hadin gwiwa da ke tsakaninsu shi ne kawo wa jama'ar kasashen biyu moriya. Ko shakka babu, kasashen biyu za su sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasa tare da kawo wa jama'ar kasashen biyu alheri, ta hanyar yin amfani da kasuwar Sin da kimiyyar Jamus. Kuma hada saurin bunkasuwar Sin da ingancin kayayyakin Jamus tare, zai baiwa tattalin arzikin Sin da Turai karfi da makoma mai haske wajen samun bunkasuwa, har ma ga duniya baki daya.
Ban da haka kuma, Sin da Jamus kasancewarsu kasashen da suke bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, hadin gwiwar da ke tsakaninsu za ta yi amfani sosai wajen gaggauta samar da madogara ga duniya, da ma kiyaye zaman lafiyar duniya mai karko da wadata. (Amina)