in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Faransa sun yi alkawarin bude wani sabon shafi na hulda tsakanin kasashensu
2014-03-28 09:02:27 cri

Shugaban kasar Sin, Xi Jinping da takwaransa na kasar Faransa, Francois Hollande, a jiya Alhamis ne suka yi amanna a bisa cewar za su bude wani sabon lale, na huldar kasa da kasa.

Shugabannin kasashen biyu sun dauki wannan alkawarin ne, a yayin wani taro da aka shirya domin tuna zagayowar ranar cika shekaru hamsin ta kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Shugaban kasar ta Sin, ya ba da shawara a kan cewar, kasashen biyu su ci gaba da karramawa, tare da amincewa da juna, da kuma jajircewa wajen raya hulda ta kasa da kasa, a bisa turba ta kwarai da kuma goyon bayan kokarin da suke yi na tsare manyan bukatun juna, a bangaren 'yancin kai, tsaro da kuma ci gaban kasashe, tare kuma da karfafa manyan batutuwa da gamayya da juna.

Xi, ya ci gaba da shawarta cewar, kasashen biyu su ci gaba da aiki da gaskiya, da kuma habbaka kasuwanci, tare da kaucewa takunkumi na cinikayya, da kuma inganta tsarin manufofi na tattalin arziki, tare da zaburar da canje-canje a tsarin tattalin arziki da hada-hadar tafiyar da kudade na duniya da zummar bunkasa tattalin arziki na duniya.

Shugaban kasar ta Sin ya kuma jaddada cewar, kasashen Sin da Faransa za su inganta tsarinsu na tafiyar da harkokin da suka shafi yankunansu, tare da hade karfi wajen fuskantar kalubale na duniya, ta yadda huldar Faransa da Sin za ta zamanto wani ginshiki na samar da zaman lafiya da ci gaban bil Adama.

Shi a yayin da yake jawabi ga taron, shugaban kasar Faransa Hollande, ya ce, kasashen biyu suna bisa turbar samar da canje-canje da sabbin dabaru, kuma hakan ya sa sun samar wa juna gurabuna na bunkasa, a inda ya kara da cewar, kasar Faransa a shirye take ta habbaka hadin gwiwa da kasar Sin. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China