Bisa gayyatar da Asusun Korber na kasar Jamus ta yi masa ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da wani muhimmin jawabi a birnin Berlin a ran 28 ga wata da yamma, inda ya bayyana hanyar neman ci gaba cikin zaman lafiya da kuma manufar diflomasiyyar bisa zaman lafiya cikin 'yancin kai ta kasar Sin, inda ya kuma jaddada cewa, babban dalilin neman ci gaban kasa ta hanyar zaman lafiya ya dace da al'adun jama'ar kasar Sin na kaunar zaman lafiya, kuma abu mai ma'ana shi ne, darussan da jama'ar kasa suka koyo daga tarihi, lamarin da ya dace da halayen jama'ar kasar Sin. Don haka, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen neman ci gaban kasa ta hanyar zaman lafiya, kuma tana fatan kasa da kasa za su yi koyi da wannan hanya wajen neman bunkasuwa.
Bayan ya kammala jawabinsa, shugaba Xi ya kuma amsa wasu tambayoyin da aka yi masa. (Maryam)