Yau ranar Alhamis 27 ga wata, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi jawabi a babban zauren hukumar kula da tarbiya da kimiyya da al'adu ta MDD wato UNESCO da ke birnin Paris na kasar Faransa, inda ya yi cikakken bayani kan ra'ayinsa dangane da yin mu'amala da yin koyi da juna a tsakanin al'adu daban daban, sannan ya jaddada cewa, ya kamata a kara azama kan tabbatar da girmama juna da yin zaman tare cikin jituwa a tsakanin al'adu daban daban, a kokarin ganin yin mu'amala da yin koyi da juna ta fuskar al'adu sun taimaka wajen kara dankon zumuncin da ke tsakanin al'ummomin kasa da kasa, sa kaimi kan ci gaban zaman al'ummar dan Adam, da kiyaye zaman lafiya a duk duniya. (Tasallah)