in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da firaministan Burtaniya
2014-03-25 20:36:02 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Burtaniya David Cameron a kasar Holland a yau Talata 25 ga wata.

A lokacin ganawarsu, Shugaba Xi Jinping ya ce, kasar Sin na fatan za a iya ci gaba da shawarwari da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, tare da fahimta da girmama juna. Sannan ya kamata kasashen biyu su karfafa hadin gwiwar a fannonin ba da ilmi, kimiyya da fasaha, kafofin watsa labarai da dai sauransu.

Mr. Xi ya kara da cewa, kasar Sin tana girmama muhimmin matsayin kasar Burtaniya a kungiyar tarayyar kasashen Turai, don haka tana fatan kasar Burtaniya za ta taimaka wajen ciyar da kafuwar yankin ciniki maras shinge dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai gaba.

A nasa bangaren, firaminista David Cameron ya bayyana cewa, kasar Burtaniya na dukufa wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasarsa, kuma tana son dukufa tare da kasar Sin wajen ciyar da shawarwarin dake tsakanin shugabannin kasashen biyu gaba, tare da raya manyan harkokin zuba jarin dake tsakanin kasashen biyu.

Ya ce kasar Burtaniya tana goyon bayan kasar Sin wajen kulla yarjejeniyar zuba jari tsakanin kasar Sin da kasashen Turai cikin sauri, sannan tana son taimakawa ganin an kafa yankin ciniki maras shinge a tsakanin kasar Sin da kasashen Turai yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China