in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya halarci taron koli na tabbatar da tsaron makamashin nukiliya karo na uku
2014-03-25 10:58:15 cri

An shirya taron koli na tabbatar da tsaron makamashin nukiliya karo na uku a ran 24 ga wata a birnin Hague na kasar Holand. Shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya halarci taron tare da gabatar da wani muhimmin jawabi, inda ya bayyana matakan da Sin ta dauka na tabbatar da tsaron nukiliya da sakamakon da ta samu, tare da gabatar da ra'ayin kasar Sin kan tabbatar da tsaron makamashin nukiliya wanda ya hada da raya shi tare da tabbatar da tsaronsa, Sin na da iko da nauyin da ke bisa wuya, wajen gudanar da aiki bisa karfin kanta tare da hadin kai da sauran kasashe, da kuma daidaita matsaloli dangane da makamashin nukiliya na yanzu tare da kawar da tushen matsalolin, Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su hada kansu, domin cimma burin raya makamashin nukiliya cikin tsaro kuma cikin dogon lokaci.

Babban taken taron kolin wannan karo shi ne, 'karfafa tsaron nukiliya, da hana amfani da makaman wajen aikata ta'addanci', shugabanni da wakilai daga kasashe 53 da jami'an kungiyoyin duniya da dama sun halarci taron. Firaministan kasar Holand Mark Rutte ya jagoranci taron, inda kuma ya gayyaci shugaba Xi Jinping gabatar da wani jawabi da ke jaddada babban taken taron.

A nasa jawabin, shugaba Xi ya yi nuni cewa, idan 'yan Adam suna son kara yin amfani da makamashin nukiliya yadda ya kamata don kara samun cigaba, wajibi ne su tinkara kalubaloli da dama, da tabbatar da tsaro na kayayyakin makamashin da na'urorinsa. Inganta tsaron nukiliya ya zama wani aiki ne da ake gudanar da shi cikin dogon lokaci. Kamata ya yi mu tsaya tsayin daka kan ra'ayin bin gaskiya da samun daidaito da cigaba tare, da mayar da aikin tabbatar da tsaron makamashin nukiliya cikin hanyar da muke bi ta samun bunkasuwa mai karko yadda ya kamata.

Xi ya karfafa cewa, kasar Sin ta rike tarihi mai kyau a cikin shekaru fiye da 50 da ake raya makamashin nukiliya. Sin ta gudanar da bincike daga dukkan fannoni kan na'urorin nukiliya a duk fadin kasar, tare da kara kyautata ka'idojin da abin ya shafa, a yanzu haka tana kokarin tsara dokoki don tabbatar da tsaro. Ban da wannan kuma, kasar Sin ta sa kaimi ga kasa da kasa da su hada kai a fannin tabbatar da tsaron makamashin nukiliya. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China