Shugaba Xi tare da uwargidansa Peng Liyuan, sun isa filin jirgin saman Schiphol dake Amsterdam ne a jiya Asabar, da karfe 12 da rabi na rana bisa agogon birnin, inda sarkin kasar Holland Willem Alexander da uwargidansa Maxima Cerruti suka tarbe su da hannu bibbiyu.
Ana sa ran shugaba Xi zai halarci babban taron tsaron makamashin nukiliya karo na uku da za a yi a birnin Hague, inda zai bayyana ra'ayin kasar Sin kan tsaron makamashin nukiliya, zai kuma gana da wasu shugabannin kasashen duniya.
Baya ga kasar Holland, shugaban kasar ta Sin zai kuma ziyarci kasashen Faransa, da Jamus, da Belgium, da kuma hedkwatar UNESCO, wato hukumar bunkasa ilmi da al'adu da kimiyya ta MDD, da hedkwatar kungiyar tarayyar kasashen Turai ta EU. (Maryam)