in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya gana da babban sakataren MDD kan batun Ukraine
2014-03-24 10:52:23 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da sakatare janar na MDD Ban Ki-moon a ranar Lahadi a birnin Noordwijk na kasar Netherlands, inda suka yi musanyar ra'ayoyi kan rikicin kasar Ukraine. Mista Ban ya sanar ga shugaban kasar Sin kan kokarin baya bayan nan da MDD ta yi wajen warware rikicin kasar Ukraine.

Mista Xi ya bayyana cewa, rikicin kasar Ukraine ya nuna karara cewa, ya shafi moriyar da damuwar dukkan bangarorin da wannan rikici ya shafa, ya kamata a warware wannan rikici cikin adalci, in ji shugaban Xi Jinping.

Kasar Sin ta gabatar da wata mafita zuwa kashi uku domin sulhunta wannan rikici, tare da fatan dukkan bangarorin da rikicin ya shafa za su nemo bakin zaren warware wannan matsala cikin hadin gwiwa domin kaucewa daukar makamai, in ji shugaban kasar Sin, tare da kara bayyana cewa, a halin yanzu magana ta gaggawa ita ce ta lalubo bakin zaren warware wannan rikici.

Haka kuma mista Xi ya yaba da kokarin shiga tsakani da shugaban MDD ke yi kan wannan batu da kuma bayyana goyon bayansa kan muhimmin matsayin da MDD take dauka domin bunkasa mafitar siyasa kan wannan rikici.

A yayin da yake fatan ganin an cimma wata mafita kan rikicin kasar Ukraine ta hanyar shawarwari, mista Ban ya bayyana cewa, kasar Sin, mambar din din din ta kwamitin tsaro na MDD, tana taka muhimmiyar rawa wajen aikin sulhunta rikici ta hanyar siyasa da shawarwari. Ya ce, zai cigaba da rike hanyar tattaunawa tare da kasar Sin kan wannan batu.

Mista Xi Jinping da Ban Ki-moon suna kasar Netherlands domin halartar taro karo na uku kan batun tsaron nukiliya da zai gudana a birnin Haye daga ranar Litinin zuwa ranar Talata. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China