Shugaban kasar Sin ya tashi don halartar taron koli karo na uku kan tsaron nukiliya tare da shirin ziyartar wasu kasashen Turai hudu
Shugaban kasar Sin Mr Xi Jinping ya tashi a safiyar yau Asabar 22 ga wata domin halartar taron koli karo na uku dangane da tsaron nukiliya bisa gayyatar da firaministan kasar Holland Mark Rutte ya yi masa. Ban da haka kuma, Mr Xi zai kai ziyarar aiki a kasashen Holland, Faransa, Jamus da Belguim bisa goron gayyartar wadannan shugabannin kasashen hudu, wato sarkin Holland Willem Alexander, shugaban Faransa Francois Hollande, shugaban Jamus Joachim Gouck da shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel da kuma sarkin Belguim Philippe Leopold Louis Marie. Haka kuma, zai ziyarci hedkwatar kungiyar UNESCO bisa gayyatar babban jami'ar kungiyar Irina Bokova, tare da kai ziyara a hedkwatar kungiyar kawancen kasashen Turai EU bisa gayyatar shugaban EU Herman Von Rompuy.
Masu rufe shugaban Xi baya a wannan ziyara sun hada da matarsa Peng Liyuan, da wasu sauran manyan kusoshin kasar. (Amina)