Shuwagabannin sun cimma wannan kuduri ne yayin ganawar da suka yi a yau Lahadi, a ci gaba da ziyarar aiki da shugaba Xi ke yi a kasar ta Netherlands.
Wata sanarwar hadin gwiwa da shuwagabannin biyu suka fitar ta ce ana fatan daukar wannan mataki, zai ba da damar gudanar da budaddiyar hadin gwiwa tsakanin sassan bBiyu, a ci gaba da fadada dangantakar Sin, da mahukuntan take kokarin yi da ragowar kasashen Turai. (Saminu Hassan)