Shugabannin kasashen Sin da Amurka sun bayyana ra'ayoyinsu a ranar Litinin a birnin Hague domin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen nasu biyu wajen yaki da ta'addanci da manyan laifuffukan kasa da kasa.
A yayin wata ganawa da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama a yayin taron tsaron nukiliya a birnin Hague, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, yana yabawa sosai da matsayin da Obama ke dauka wajen yin allahwadai da duk wani nau'in ta'addanci, kuma kasar Sin a shirye take wajen yin aiki tare da dukkan kasashe, har ma da Amurka domin yaki da ta'addanci.
Mista Xi ya kuma yi kira da a karfafa hadin gwiwa tsakanin 'yan sandan kasar Sin da na Amurka a cikin fannonin da suka hada da yaki da manyan laifuffukan kasa da kasa, da kuma farautar da mutanen da suke gujewa gurfana gaban kuliya.
A nasa bangare, mista Obama ya jaddada matsayinsa na yin allahwadi da harin ta'addancin da ya faru a birnin Kunming dake kudu maso yammacin kasar Sin, tare da bayyana cewa, kasarsa na adawa da duk wani nau'in ta'addanci, kuma yana allahwadai da duk wasu ayyukan ta'addanci a duk inda suka faru.
Kasar Amurka a shirye take ta karfafa hadin gwiwa wajen yaki da ta'addanci tare da kasar Sin, in ji Barack Obama. (Maman Ada)