in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da takwaransa na Amurka a birnin Hague
2014-03-24 21:04:43 cri

A yau Litinin ranar 24 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama sun gana a birnin Hague na kasar Holland, inda shugaba Xi Jinping ya mika godiya ga shugaba Obama dangane da wayar da ya buga masa, don nuna juyayi ga kasar Sin kan jirgin saman Malaysian da ya bace, da kuma taimakon da kasar Amurka ta baiwa kasar Sin wajen binciken jirgin saman.

Mr. Xi ya ce, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasar Amurka wajen raya dangantakar kasashen biyu yadda ya kamata, kuma kasar Sin za ta ci gaba da rike da manufofinta na girmama juna, yin hadin gwiwa tare da cimma moriyar juna.

Haka kuma in ji Shugaba Xi kasar Sin za ta dukufa wajen karfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu kan harkokin kasa da kasa da kuma na shiyya-shiyya, don warware rikice-rikice ta hanyoyin da za su dace, ta yadda za a iya inganta dangantakar kasashen biyu yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China