A gun bikin sa hannu, tarrayar Rasha ta fara aikin kyautata yankin Crimea, ta yadda za a taimakawa wannan yanki domin ya shiga ciki tsarin doka, tattalin arziki da al'umma na tarayyar.
A wannan rana kuma, Putin ya tattauna da mambobin kwamitin tsaro na tarayyar kan yadda za a tinkarar takunkumi daga waje. Inda ya nuna cewa, ya kamata Rasha ta nuna karfinta wajen daidaita takunkumi da za a sanya mata.
Babban magatakardan MDD Mr Ban Ki-Moon wanda ya kai ziyara a kasar Ukraine ya bayyana a ran 21 a birnin Kiev cewa, daidaita rikicin dake tsakanin Ukraine da Rasha kan Crimea cikin lumana kasancewar hanya daya kacal ne. Kuma ya kara da cewa, ya kamata, bangarorin biyu su kaucewa daukar matakin takala wanda zai tsanantar da halin da ake ciki, ya jaddada cewa, kamata ya yi, kasashen biyu su yi shawarwari masu amfani.
Mukadashin shugaban kasar Ukraine Alexander Tyrchinov ya ce, kasar na yin shirin shawarwari da Rasha. Kuma yana fatan MDD ta goyi bayan shawararsa na kafa yankin babu soja a Crimea ta yadda za a sa kaimi ga wanzar da zaman lafiya a tsibirin. (Amina)