Yau Alhamis 13 ga wata, majalisar dokokin Ukraine ta kira cikakken taronta karo na biyu a wannan mako, inda aka zartas da shirin dokar maido da rundunar tsaron jama'a da kuma tabbatar da manufarta ta hadewa da kasashen Turai. Majalisar ta kuma yi kira ga kasashe mambobin MDD da su tabbatar da tsaron Ukraine ta fuskar siyasa da tattalin arziki, da kuma hana kasar Rasha ta yi mata katsalandan.
Haka zalika, Arseniy Yatsenyuk, firaministan Ukraine na wucin gadi da ke ziyara a kasar Amurka ya samu goyon baya daga kasar ta Amurka sosai. Ban da haka kuma, a wannan rana, majalisar kungiyar tarayyar Turai ta yi wani taro, inda ta hanyar jefa kuri'a aka amince da shawarar da aka gabatar dangane da bai wa Ukraine tallafin kudi. (Tasallah)