Yayin da ke jawabi ga jama'ar kasar Ukraine a wannan rana, Mr. Turchynov ya bayyana cewa, kasar za ta yi kokarin kaucewa yake-yake ko asarar rayuka, jikkatar mutane, amma kasar na fuskantar kalubalen soja, shi ya sa, ya sanya hannu kan wata dokar daukar sojoji daga wasu yankunan kasa, a halin yanzu, majalisar dokokin kasar ta zartas da dokar, inda jama'ar kasar da dama suka nuna anniyarsu ta shiga aikin soja don kare kasarsu.
Mr. Turchynov ya ce, kasar Ukraine na shirya yin shawarwari tare da bangarorin da abin ya shafa dangane da batun yankin Crimea, kuma kasar Ukraine ba za ta amince da kuri'ar raba gardamar da aka kada game da makomar Crimea ba.
Bugu da kari, a ran 17 ga wata, ma'aikatar harkokin wajen kasar Ukraine ta sanar da cewa, dangane da matsayin da yankin Crimea ya dauka na komawa kasar Rasha, ya kamata a tattauna tare da bangarorin da abin ya shafa game da wasu batutuwa, kuma kasar ta dawo da jakadanta dake tarayyar Rasha Vladimir Yelichenko don tattaunawa kan batu. (Maryam)