A ran 18 ga watan Maris ne bisa, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugabannin Jamhuriyar Crimea da birnin Sevastopol sun daddale yarjejeniyoyin shigar da wuraren biyu a cikin Jamhuriyyar tarayyar Rasha.
Putin ya yi jawabi a gun taron majalisar tarayyar kasar cewa, kada kuri'ar raba gardama a Crimea ta dace da ajandar dimokuradiyya da ka'idojin dokokin duniya. Ya yi kira ga MDD da Amurka da su amince da sakamakon kada kuri'ar da aka yi a Crimea bisa ga misalin da abin da ya faru a da, a Kosovo.
Game da jawabin Putin, ma'aikatar harkokin wajen Ukraine, ta bayar da wata sanarwa a ran 18 ga wata cewa, Ukraine ta nuna babbar adawa ga Rasha da ta amince da Jamhuriyar Crimea, kasar Ukraine ba ta amince da Crimea ta shiga cikin tarayyar Rasha ba, kuma za ta dauki dukkan matakai bisa dokokin duniya don maido da kasar Ukraine da ta zama kamar yadda take a da.
Shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya buga waya ga shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel kan halin da ake ciki a Ukraine a ran 18 ga wata, inda shugabannin biyu suka kai suka akan Kasar Rasha wacce ta daddale yarjejeniyoyin na shigar da Crimea da Sevastopol a cikin tarayyar Rasha. (Danladi)