'yan majalissar sun amince da samar da 'yancin ne a lokacin wani zama na musamman,inda suka ayyana babban yankin dake shiyan tekun black sea a matsayin jiha mai cikakken 'yancin kuma jamhuriyar Crimea.
Wannan sanarwar ya bukaci Majalissar Dinkin Duniya da kasashe mambobinta su shaida wannan 'yanci, tare da alkawarin inganta zumunci da sauran kasashe bisa daidaici da mutunta juna,zaman lafiya da makwabtaka mai karko tare da sauran dangantaka na siyasa,tattalin arziki da al'adu wanda aka amince dashi a duniya baki daya.
'yan majalissar sun kuma aika a hukumance da wasika ga gwamnatin kasar Rasha ta neman iznin komawa karkashin inuwar Tarayyar Rasha a matsayin sabuwar Jamhuriya. (Fatimah Jibril)