Yayin da suke tsokaci kan kuri'ar raba gardamar da yankin Crimea ke shirin gudanarwa, Mr. Putin ya bayyana cewa, kudurin da yankin na Crimea zai cimma bayan kammala kuri'ar raba gardamar, ya dace da dokokin kasa da kasa, da na kasashe masu ruwa da tsaki, da ma kundin tsarin MDD.
Har ila yau, mataimakin babban sakatare mai kula da kare hakkin dan Adam na MDD, Ivan Simonovic, ya bayyana cewa, MDD za ta gaggauta aikewa da tawagar sa ido, domin nazartar batun kare hakkin dan Adam a kasar ta Ukraine, da yankin Crimea, da kuma ba da taimakon sassauta yanayin tashin hankali a yankin.
Bugu da kari, a yayin taron gaggawar da kwamitin tsaron MDD ya kira a ranar 13 ga watan nan, firaministan kasar ta Ukraine ya yi watsi da matsayar kasar ta Rasha bisa dogaronsa ga kundin tsarin MDDr.
Bisa kudurin da majalisar dokokin yankin Crimea ta fitar dai, za a gudanar da kuri'ar raba gardama game da matsayin yankin ne a gobe Lahadi. Duk kuwa da cewa tuni gwamnatin kasar Ukraine ta sanar da haramcin wannan kuri'ar. Baya ga kasashen yammacin duniya da dama, da suka hada da Amurka, da Burtaniya da dai sauransu, dake bayyana rashin amincewa da gudanar wannan kuri'a.
Sai dai a nata bangare kasar Rasha, ta bayyana cewa, za ta girmama, tare da goyon bayan sakamakon kuri'ar da jama'ar yankin na Crimea za su kada. (Maryam)