Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya buga waya ga takwaransa na kasar Amurka Brack Obama da tsakar daren jiya Lahadi 16 ga wata inda Putin ya nanata cewa, kada kuri'ar raba gardama a jamhuriyar Crimea da ke da ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Ukraine ta dace da ka'idojin dokar kasashen duniya da tsarin mulkin MDD.
Yayin da suke magana, Putin ya ce, ta hanyar kada kuri'ar raba gardama, jama'ar yankin Crimea sun tabbatar da 'yancinsu da yiyuwar amincewa da makomarsu. Putin ya kara da cewa, mahukuntan Ukraine ba su da kwarewa kuma ba su nuna aniyarsu ba wajen daina ayyukan sabawa dokoki da masu ra'ayin gani-kashe-ni na kabilu da kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi suka gudanar, wadannan mutane sun illa ga zaman lafiya, tare da tsoratar da fararen hula ciki har da 'yan kabilar Rasha.
Game da wannan halin da ake ciki, an ce, bangarorin Amurka da Rasha sun yi la'akari da tura tawagar sa ido ta kungiyar tsaro da hadin kai ta Turai. Game da hakan, Putin ya ce, kamata ya yi a kara fadin aikin tawagar a duk yankin Ukraine. Shugabannin biyu sun yi nuni da cewa, ko da yake bangarorin biyu suna da bambancin ra'ayoyi, amma tilas ne su yi kokari tare wajen neman hanyar da ta kamata a bi wajen shimfida zaman lafiya a kasar Ukraine.
Yayin da yake zantawa da wakilin tashar talibijin na kasar Rasha, shugaban majalisar wakilai ta kasar Rasha Sergey Naryshkin ya bayyana cewa, kada kuri'ar raba gardama a jamhuriyar Crimea mai ikon tafiyar da harkokin kanta ba ta zama wani muhimmin lamari a tarihinsa kawai ba, a'a, tana da muhimmanci ma sosai ga kasar Rasha. Kuri'un da jama'a da yawa suka jefa sun bayyana burin jama'ar daga dukkan fannoni. (Danladi)