Yanukovych ya bayyana hakan ne yau ga manema labarai a garin Rostov-on-Don da ke kudu maso yammacin kasar Rasha, inda ya ce, har yanzu shi ne halalttacen shugaban kasar ta Ukraine, kana kwamandan askarawan kasar, amma wasu da ya kira, masu yunkurin amfani da ayyukan ta'adanci suka tilasta masa barin kasar.
Bugu da kari ya ce, zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa a watan Mayu haramtacce ne. Ya ce, da zarar al'amura sun inganta zai dawo Kiev, babban birnin kasar ba da dadewa ba.
Amurka dai ta yi shirin baiwa kasar ta Ukraine tallafin dala biliyan 1, matakin da a cewar Yanukovych ya saba wa dokar kasar ta Amurka. (Ibrahim Yaya)