Kudurin ta bayyana cewa, yankin na Crimea zai zama mai cin gashin kansa idan har mutane miliyan 2 da ke zaune a yankin suka kada kuri'ar amincewar yankin na komawa kasar Rasha a kuri'ar raba gardamar da za a kada ranar Lahadi mai zuwa.
A ranar Alhamis ne, majalisar dokokin yankin na Crimea ya kada kuri'ar amincewa da komawa kasar Rasha, ko da yake hukumomin Ukraine sun yi watsi da kuri'ar raba gardamar da yankin ke shirin kadawa, matakin da suka ce ya saba wa doka.
A ranar Jumma'a kuma kakakin majalisar dokokin Ukraine Alexandr Turchynov, kana mai rikon mukamin shugaban kasar, ya sanya hannu kan dokar da ta haramta wa 'yan majalisun dokokin yankin na Crimea kada kuri'ar raba gardamar da suke shirin kadawa, inda suka yi barazanar rusa majalisar yankin na Crimea. (Ibrahim)