in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Ukraine ya halarci taron gaggawa na kwamitin sulhu na MDD
2014-03-14 11:21:28 cri

Firaministan kasar Ukraine Arseniy Yatsenyuk ya halarci taron gaggawa da kwamitin sulhu na MDD ta yi kan halin da kasar ta Ukraine ke ciki a ran Alhamis 13 ga wata, a cikin jawabinsa lokacin ya bayyana halin da kasar ke ciki yanzu, tare kuma da zargi kan matakin da Rasha ta dauka yana mai cewa, wannan hari ne da Rasha ta kai ma kasarsa. Mr Yatsenyuk kuma ya nanata musanta shawarar da aka yanke ta shigar da Crimea a tarrayar Rasha, sannan ya nemi da a janye sojojin Rasha daga tsibirin Crimea.

Zaunannen wakilin Rasha dake MDD Culkin Vidalin Ivanovich a cikin jawabinsa ya nanata cewa, hambarar da gwamnati da karfin tuwo haramtaccen mataki ne, don haka jama'ar Crimea na da hakkin zabar hanyar da za su bi nan gaba.

Sakataren harkokin waje na kasar Amurka John Kerry ya bayyana a wannan ranar cewa, idan Rasha ba za ta nuna niyyarta na warware batun zaben raba gardama a yankin Crimea ba, Amurka da kungiyar kawancen kasashen Turai EU za su dauki matakai masu tsanani a kanta bisa sakamakon zaben da za a gabatar a ran 17 ga wata.

Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana a lokacin zaman na kwamitin sulhu na MDD cewa, Sin na yin daidaici da adalci kan batun Ukraine, don haka tana fatan bangarorin da wannan abun ya shafa za su yi shawarwari da sulhunta a tsakaninsu, ta yadda za su daidaita bambancin ra'ayi bisa moriyar jama'ar Ukraine da wanzar da zaman lafiyar a kasar. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China