Amma duk da haka, zaunannen wakilin kasar Faransa da ke MDD na ganin cewa, ya kamata a ci gaba da gudanar da irin wannan taro, a kokarin warware rikicin da ake fuskanta yanzu cikin ruwan sanyi.
A wannan rana, Ban Ki-moon, babban sakataren MDD ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su ci gaba da kokarinsu wajen lalubo kyakkyawar hanyar warware rikicin a siyasance cikin dogon lokaci, da kuma taimakawa Ukraine wajen sassauta zaman dar-dar a kasar.
A wata sabuwa kuma, a ranar 13 ga wata, Arseniy Yatseniuk, firaministan Ukraine na wucin gadi zai yi jawabi a taron kwamitin sulhu, inda zai yi karin bayani kan halin da kasarsa ke ciki. (Tasallah)