Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mr. Qin Gang, ya ce kasar Sin ta kauracewa kada kuri'a, kan daftarin kudurin da kwamitin sulhun MDD ya gabatar don gane da batun yankin Crimea na kasar Ukraine.
Mr. Qin wanda ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin manema labaru kan wannan batu, ya kara da cewa, daftarin kudurin da aka gabatar a jiya Asabar, gaban wakilai mambobin kwamitin na sulhu, na iya janyo sa in sa, tsakanin bangarori daban-daban, wanda hakan ka iya tsananta halin da ake ciki a yanzu.
Don hake ne a cewar sa, kasar Sin ta bukaci bangarorin da lamarin ya shafa, da su kai zuciya nesa, tare da dora muhimmanci kan warware wannan batu ta hanyar siyasa.
Mr Qin ya kara da cewa, Sin ba ta kada kuri'ar ta ba, kan daftarin da kwamitin tsaron ya fitar game da shirin gudanar da zaben raba gardama a yankin na Crimea. Kuma bayan kada kuri'ar, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi, ya bayyana matsayin Sin kan hakan, inda ya ce kasar sa, na mutunta ikon mulkin yankunan ko wace kasa, wanda hakan ya kasance manufa mai tushe, da Sin ke dauka kan kasashen waje.
Ya kara da cewa kasar Sin, ta yi imanin halin da Ukraine ke ciki, na da alaka da dalilin tarihi da na yanzu, kuma kamata yayi a daidaita wannan batu tare da yin la'akari da hakan. Haka zalika Sin, ba za ta yarda da daukar duk wani mataki na nuna kiyayya ga wani bangare ba.
Har ya zuwa wannan lokaci, Sin na kira ga bangarori daban-daban, da su yi hakuri da juna, domin kaucewa kara tsanantar halin da ake ciki, a kuma yi iyakacin kokarin warware matsalar ta hanyar siyasa.
Dadin dadawa, Mr Qin ya ce, Sin na daukar matsayi madaidaici bisa adalci kan wannan batu, kuma za ta ci gaba da sa kaimi ga yin shawarwari, da daidaita batun ta hanyar siyasa. Tuni dai kasar ta Sin ta gabatar da shawararta, ciki hadda bayyana muhimmancin kafa wani tsari na kasa da kasa, wanda zai nazarci hanyar da ya dace kasar Ukraine ta bi a nan gaba.
Daftarin kudurin da Amurka ta gabatar a ranar Asabar 15 ga wata, kan batun kasar ta Ukraine dai bai samu nasara ba, saboda hawa kujerar naki da Rasha ta yi kan lamarin. (Amina)