Bisa labarin da kafofin yada labaru na Rasha suka bayar, an ce, a safiyar yau ne Ban Ki-moon ya isa birnin Moscow. Yayin ziyarar tasa ta yini guda, zai yi shawarwari da shugaban Rasha, Vladimir Putin, da ministan harkokin wajen kasar, Sergey Lavrov, da wasu manyan jami'an kasar kan yanayin da ake ciki a Ukraine, a kokarin shiga tsakani don daidaita rikicin Ukraine ta hanyar diplomasiya. Daga bisani, Ban Ki-moon zai tashi zuwa Kiev,babban birnin kasar Ukraine domin yin shawarwari da shugabannin wurin. Kafin wannan, kakakin Ban Ki-moon ya furta cewa, makasudin ziyararsa a wannan karo, shi ne sa kaimi ga Rasha da Ukraine da su yi shawarwari tsakaninsu kai tsaye, a kokarin cimma matsaya kan wasu hakikanin matakan da za a dauka.
Wani manazarcin Rasha yana ganin cewa, ziyarar Ban Ki-moon a wannan karo za ta bude wani sabon babi na kokarin shiga tsakani kan batun rikicin Ukraine. Ya yi hasashen cewa, yayin shawarwarin, Rasha za ta bayyana wa Ban Ki-moon cewa, matsayin da Rasha ke kasancewa na amincewa da shigar da Crimea cikin kasar na bisa doka, kuma ya dace da wasu sassan dokokin kasa da kasa.(Fatima)