in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Rasha ta zartas da dokokin komawar Crimea karkashin kasar
2014-03-21 10:49:23 cri
A ran 20 ga wata, majalisar dokokin kasar Rasha ta Duma, ta zartas da dokokin da suka shafi komawar Crimea da birnin Sevastopoli karkashin ikon kasar, lamarin ya sanya Amurka da kasashen Turai kakabawa kasar ta Rasha sabbin takunkumi.

A wannan rana, an kada kuri'u a majalisar Duma ta kasar Rashan, inda aka zartas da yarjejeniyar komawar Crimea da birnin Sevastopoli karkashin Rasha, da kuma daftarin tsarin mulki game da matsayin sabbin mambobin tarayyar kasar, da kuma batun kan iyaka da dai sauransu.

Dangane da wannan lamari, majalisar dokokin kasar Ukraine ta fidda wata sanarwa, inda ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su bayyana rashin amincewa da komawar Crimea da Sevastopoli karkashin kasar ta Rasha.

Har wa yau babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya fara wani shiri na shiga tsakani cikin gaggawa, inda ya tashi zuwa Moscow, babban birnin kasar Rasha, kuma ya tattauna da shugaba Vładimir Putin na Rasha, da kuma ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov jiya ranar 20 ga wata.

Wannan rana, kungiyar tarayyar kasashen Turai ta fara taron kolinta na lokacin bazara, inda shugabannin kasashe 28 ke tattaunawa kan yadda za a tsara aiwatar da takunkumi ga Rasha.

Bugu da kari, shugaba Barack Obama na Amurka, ya sanar da cewa, kasarsa za ta kakaba wa manyan masana'antun kasar Rasha takunkumi, kana cikin jerin takunkumin da ma'aikatar harkokin kudin kasar Amurka ta fitar, akwai sunan wani babban darekta a ofishin shugaba Putin, da wasu manyan jami'an kasar da jimillarsu ta kai mutane 20.

A nata martani kan sabbin takunkumin da kasashen Turai da Amurka suka fitar, ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha ta sanar da kakaba wa manyan jami'an gwamnatin kasar Amurka, da kuma mambobin majalisar dokokin kasar Amurka da jimillar su ta kai mutane 9 takunkumi, na haramta musu shiga kasar ta Rasha. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China