in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Koton tsarin mulkin Rasha ta tabbatar da yarjejeniyar komawar Crimea karkashin Rasha
2014-03-20 15:00:23 cri
Jiya Talata 19 ga wata, koton tsarin mulkin tarayyar kasar Rasha ta tabbatar da cewa, yarjejeniyar da Crimea da kuma birnin Sevastopol suka kulla kan komawarsu karkashin ikon Rasha ta dace da tsarin mulkin kasar.

A wannan rana, majalisar dokokin kasar Rasha wato Duma ta bayyana cewa, shugaba Putin ya riga ya gabatar da yarjejeniyar da koton tsarin mulkin kasar ta zartas da kuma daftarin tsarin mulki dake da alaka da wadannan sabbin yankuna biyu ga majalisar dokoki.

Ana sa ran majalisar ta Duma za ta kammala nazari kan yarjejeniyar da daftarin ya kunsa cikin makon nan da muke ciki. A sa'i daya kuma, kasar Rasha na nazartar yanayin zamantakewar al'umma bayan komawar Crimea karkashinta.

Haka nan a wannan rana Shugaba Putin ya jagoranci taron gwamnati, inda ya bukaci ministan kula da harkokin kwadago da ba da tabbaci kan zaman takewar al'umma, da ya gaggauta daukar matakan da suka dace don kyautata matsayin kudin ritayar al'ummar yankin Crimea, yadda zai dace da matsayi irin na kasar Rasha.

Haka zalika, sakataren kwamitin kula harkokin tsaron kasar Ukraine ya bayyana a dai wannan rana cewa, kwamitin ya riga ya mika wata bukata ga ma'aikatar harkokin wajen kasar, kan samar da tsarin biza ga al'ummar tarayyar kasar Rasha. Bisa tsarin, dukkanin 'yan kasar ta Rasha sai sun mallaki biza kafin su iya shiga kasar Ukraine.

A wani ci gaban kuma, kakakin gwamnatin kasar Jamus ya bayyana cewa, shugabannin kungiyar G7 za su tattauna kan hanyoyin warware rikicin kasar Ukraine, yayin taron tsaron makamashin nukiliya da za a yi a birnin Hague na kasar Holland.

Bugu da kari shi ma zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana cewa, ya kamata a warware batun Crimea ta hanyar siyasa, kuma bisa tsarin dokoki, kuma ya dace bangarorin da abin ya shafa su kwantar da hankulansu, su kaucewa daukar matakan da ba su dace ba. Ya ce kasar Sin ta riga ta bayyana ra'ayinta dangane da wannan batu, cewa za ta tsaya tsayin daka wajen girmama 'yanci kai, da cikakken ikon mulkin kai na kasa da kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China