in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi a zurfafa yin kwaskwarima a dukkanin fannoni domin cimma muradun wannan shekara, in ji firaministan Sin
2014-03-13 17:25:39 cri

Yayin taron manema labaru da aka gudanar bayan rufe zaman shekara-shekara karo na biyu, na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 12 a safiyar yau Alhamis 13 ga wata a nan birnin Beijing, inda kuma firaministan kasar Sin Li Keqiang ya amsa tambayoyin da manema labaru na gida da na waje suka yi masa. Mr Li ya yi bayani kan muradu masu wuya, da Sin take da burin cimmawa a wannan shekara da muke ciki. Muradun da suke da alaka da aniyyar Sinawa ta zurfafa yin kwaskwarima, da tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki.

Mr Li Keqiang ya nuna damuwa matuka, yayin da ya amsa tambayar da aka gabatar masa kan jirgin saman kasar Malaysiyan nan da ya bace, ya ce:

"Yanzu haka muna matukar fatan samun labari dangane da wannan lamarin. Kuma iyakacin kokarin bincike kan wasu hotuna da wata na'ura ta dauka daga sararin samaniya. Wannan aiki ya kasance wani babban matakin ceto da kasa da kasa suke gudana, kasashe da dama sun shiga aikin ceto. A namu bangare, muna fatan hukumomin da abin ya shafa, za su kara azama, wajen bincike kan dalilin aukuwar wannan hadari, da gano wannan jirgi, kuma su aiwatar da hakan yadda ya kamata. Ba za mu yi watsi da aikin ceto ba ko kadan."

Ya ce kasashen duniya na damuwa sosai, ko Sin za ta kyautata tsarin da ta dauka na bude kofa, da na sha'anin yawon shakatawa ko a'a saboda aukuwar wannan hadarin. Li Keqiang ya bayyana ra'ayinsa kan batun, ya ce, Sin za ta ci gaba da gudanar da tsarin bude kofa ga kasashen waje, ta yadda Sinawa da dama za su iya kai ziyara kasashe daban-daban. Gwamnati kuma a nata bangare, za ta yi iyakacin kokarinta domin tabbatar da tsaron jama'arta, ta hanyar kara yin hadin kai da kasashen duniya.

Tun daga shekarar 1991, taron manema labarun da firaministan kasar ta Sin ya yi, bayan babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC, na da muhimmanci sosai ga kasashen waje, wajen kimanta manufofin diplomasiyya da Sin za ta dauka.

Burin kasar Sin a wannan shekara na samun bunkasuwar tattalin aziki ya kai kimanin kashi 7.5 bisa dari, duk da cewa wasu ra'ayoyin masu zuba jari, da kafofin yada labaru na kasashen waje sun rika hasashen cewa, watakila saurin karuwar tattalin arzikin Sin zai ragu cikin sauri. Game da wannan batu, Mr Li ya nuna cewa

"Dalilin da ya sa muka saka wannan muradi na samun bunkasuwar tattalin arziki har kashi 7.5 bisa dari shi ne, domin mu tabbatar da samar da guraben aikin yi, da kara kudin shigar jama'a. Mun dora babban muhimmanci kan zamantakewar jama'a da samar da aikin yi. Wannan alkaluma ta GDP, ya kamata su tabbatar da samar da isassun guraben ayyukan yi, tare da fadada karuwar kudaden shigar jama'a. Ba wai burin mu na samu karin GDP ba ne kawai, a'a har ma da batun dora muhimmanci wajen tabbatar da moriyar jama'a, tare da kiyaye muhalli.

Rahoton da taron ministocin kudi da shugabannin manyan bankuna na kasashe mambobin kungiyar G20 ya fitar, ya kunshi wata shawara dake cewa, ya kamata a samu karuwar jamillar GDP da kashi 2 bisa dari cikin shekaru biyar masu zuwa domin kara samar da guraben aikin yi. Matakin da ya nuna cewa, wadannan kungiyoyi na mai da hankali sosai kan dangantakar dake tsakanin samun bunkasuwa da samar da guraben aikin yi."

Dadin dadawa, Mr Li ya ce, za a fuskanci kalubaloli sosai wajen tabbatar da muradun gwamnatin kasar Sin a wannan shekara, ya ce

"Ana fuskantar kalubaloli masu tsanani a wannan shekara, wadanda za su iya kara tsananta. Ya kamata mu tabbatar da samun bunkasuwa cikin karko, da tabbatar da samar da guraben aikin yi, a sa'i daya kuma mu yi rigakafin hauhawar farashin kayayyaki, da fuskantar wasu kalubaloli, da kuma tabbatar da saurin bunkasuwa mai inganci, da warware batun gurbatar muhalli. Akwai dai karin batutuwa masu iya kawo cikas. Sai dai mun yi imanin cewa za mu iya daidaita wadannan matsaloli, tare da samun bunkasuwa yadda ya kamata."

Ban da haka kuma, Mr Li ya bayyana wajibcin zurfafa yin kwaskwarima a dukkan fannoni, da tabbatar da cewa kasuwa ta yi amfani da tasirinta yadda ya kamata, tare kuma da ci gaba da aiwatar da manufar zaman tare cikin lumana, da kara yin hadin gwiwa da kasashe daban-daban. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v Kasar Sin ta dauki matakai da dama don tabbatar da samun isashen hatsi 2014-03-12 17:56:12
v An bude taron shekara shekara na CPPCC  2014-03-03 18:46:22
v Kasar Sin na mai da hankali kan ingancin abinci 2013-03-15 16:53:49
v 'Yan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin na kokarin ba da shawarwari kan gyaran tsarin rabon dukiyar al'umma 2013-03-13 18:28:00
v Sin na nacewa manufar tsaron kasa bisa kyakkyawar manufa 2013-03-12 17:11:25
v Kamata ya yi a kyautata tsare-tsare da farko yayin da ake kokarin yaki da cin hanci da rashawa 2013-03-11 17:16:57
v Sin za ta kara bude kofa ga kasashen waje tare da tabbatar da hakkin masana'antun kasar suke saka jari a kasashen waje 2013-03-08 20:42:20
v Kamata ya yi kamfanonin Sin su yi kokarin magance hadari yayin da suke aiwatar da ayyukansu a kasashen waje  2013-03-07 18:23:18
v Habaka bukatun cikin gida da kara zuba jari za su ci gaba da zama muhimman bangarori biyu dangane da raya tattalin arzikin kasar Sin  2013-03-06 18:06:49
v Kasar Sin za ta ci gaba da sanya moriyar jama'a a gaban kome yayin da take kokarin yin gyare-gyare 2013-03-05 16:39:08
v Za a fara taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin 2013-03-04 17:55:45
v Masana da fararen hula na kasar Nijeriya sun nuna kyakkyawan fata ga muhimman taruka biyu na kasar Sin 2013-03-04 11:25:48
v An bude taron shekara-shekara na majalisar CPPCC 2013-03-03 20:24:40
v Sin za ta ci gaba da yin kwaskwarima kan hukumomin majalisar gudanarwa 2013-03-01 16:04:18
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China