in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron shekara shekara na CPPCC
2014-03-03 18:46:22 cri

Ana aiwatar da manyan tsare-tsaren demokuradiya guda biyu a nan kasar Sin, ciki har da bunkasa tsarin demokuradiya ta hanyar yin shawarwari. A matsayin wata muhimmiyar hanyar tabbatar da dimokuradiya ta hanyar yin shawarwari, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin(CPPCC) na taka muhimmiyar rawa ta fuskar harkokin siyasa da zaman rayuwar jama'ar kasar.

A yau Litinin 3 ga wata ne, aka bude taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin a nan birnin Beijing, inda da farko shugabannin kasar, ciki har da shuagaba Xi Jinping, firaminista Li Keqiang da dai sauransu, da kuma mahalarta taron suka yi shiru na dan wani lokaci don nuna alhini ga wadanda suka rasa rayukansu sakamakon lamarin ta'addanci da aka kai a ranar 1 ga watan nan a birnin Kunming na lardin Yunan dake nan kasar Sin.

Daga baya kuma, shugaban majalisar mista Yu Zhengsheng ya gabatar da rahoton aiki a yayin bikin bude taron, inda ya jaddada cewa, a shekarar 2014 da muke ciki, majalisar za ta yi iyakacin kokari da nufin ba da shawarwari kan zurfafa yin gyare-gyare a dukkan fannoni a kasar, tare kuma da kara karfinta na gudanar da ayyuka, don kafa wani tsarin ba da shawara kan harkokin siyasa ta hanyar kimiyya yadda ya kamata.

A ranar 3 ga wata ne, wakilan majalisar ba da shawarwa kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin sama da 2100 suka zo taron shekara-shekara na majalisar da za a shafe kwanaki 9 ana yinsa tare da shawarwarin da za su gabatar, inda za su ba da shawarwari kan manyan manufofin da suka shafi ayyukan gyare-gyare da samun ci gaban kasar.

Shekarar da ta wuce ita ce shekara ta farko da majalisar karo na 12 ta soma gudanar da ayyukanta. Yayin da yake bayar da rahoton ayyuka ga babban taron, shugaban majalisar Yu Zhengsheng ya bayyana cewa,

"Wakilan majalisar sun bayar da wasu muhimman shawarwarin da suka danganci yin kirkire-kirkire kan fannoni guda uku wato tsarin masana'antu, da na kimiyya da fasaha, da na gudanarwa, kana da bunkasa gaurayayyen tsarin tattalin arziki, da inganta daidaituwar samun ci gaban masana'antun da gwamnati ke sa ido kansu da tsarin nazarin albashin ma'aikatan masana'antu, da dai sauransu."

A shekarar da ta gabata, wakilan majalisar, da wasu hukumomin majalisar sun gabatar da shawarwari fiye da 5000, wadanda suka shafi fannoni da dama kan yadda za a samu bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar, wadanda suka taimaka sosai ga gwamnati wajen tsara manufofin kasar. Mataimakin darektan ofishin ma'aikatar kula da harkokin albarkatun jama'a da ba da tabbaci ga zaman al'umma ta kasar Sin, Mista Zheng Xuanbo ya bayyana cewa,

"Game da batutuwan ba da tabbaci ga zaman al'umma dake jawo hankulan wakilan majalisar, mun sa himma wajen tsara tsarin inshorar tsofaffi. Kan shawarar da wakilan majalisar suka gabatar ta kara gaggauta kafa tsarin ba da tabbaci ga zaman al'umma da ya kunshi birane da kauyuka baki daya, mun yi iyakacin kokarin gudanar da ayyukan hada kan sabon tsarin inshorar manoma, da na mazauna birane. Kwanan baya, zaunannen kwamitin majalisar gudanarwa ya tsaida kudurin kafa wani hadadden tsarin inshorar tsofaffi da zai shafi mazauna kauyuka da birane baki daya."

Shekarar 2014 shekara ce ta cikon shekaru 65 da kafa sabuwar kasar Sin, kana ta cika shekaru 65 da kafa majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar. Shugaban majalisar Mista Yu Zhengsheng ya gabatar da bukatunsa game da ayyukan da majalisar za ta gudanar a shekarar.

"Za a kara bayar da shawarwari kan yadda a aiwatar da manyan matakan gyare-gyare, da yadda za a tafiyar da su, kana da inganta samun dauwamammen ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma mai jituwa yadda ya kamata, don taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tsarin demokuradiya ta hanyar tuntuba." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China