in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara bude kofa ga kasashen waje tare da tabbatar da hakkin masana'antun kasar suke saka jari a kasashen waje
2013-03-08 20:42:20 cri






Game da zancen rashin daukar sabbin matakan bude kofa ga kasashen waje, bayan da kasar Sin ta shiga cikin kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, a gun taron manema labaru dangane da taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a ranar 8 ga wata, ministan kasuwanci na kasar Sin Chen Deming ya musanta wannan zance, inda ya ce, nan gaba, kasar za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje. Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin Sin tana nuna goyon baya ga masana'antun kasar da su saka jari a kasashen waje, haka kuma za ta yi kokarin tabbatar da hakkinsu a kasashen waje.

A ranar 8 ga wata da safe, an yi taron manema labaru a cibiyar yada labaru ta majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, inda ministan harkokin kasuwanci na kasar Sin Chen Deming ya zanta da manema labaru na gida da waje game da manufar bude kofa ga kasashen waje, da sa kaimi ga masana'antu da su je su saka jari a waje, da raya sana'o'i, kana da kafa tsarin dokar sayayya a shafin Internet, bisa irin taken "Raya harkokin cinikayya ta gida da waje da sa kaimi ga hadin gwiwar tattalin arziki".

Kwanan nan, akwai wani zance da ake yadawa a kasashen duniya cewa, bayan da Sin ta shiga cikin kungiyar cinikayya ta duniya, ba ta dauki sabbin matakai na kara bude kasuwanninta ba. Yayin da Mr. Chen ke zantawa da manema labaru, ya musunta wannan zance, inda ya ce,

"'Yan shekaru 11 ke nan da muka shiga hukumar WTO har na tsawon shekaru sama da 11, mun cika alkawarin da muka dauka, haka kuma bayan da muka shiga hukumar WTO, mun kara bude kofa ga kasashen waje, mun cimma nasarar kafa yankunan cinikayya cikin 'yanci da kasashe 15, kuma a yanzu muna tattaunawa kan sabbin yankunan yin cinikayya da kasashe 13, kuma duk wadannan sun nuna cewa, muna kara bude kofa ga kasashen waje."

Chen Deming ya bayyana cewa, yayin da Sin take bude kofarta ga kasashen waje, tana fatan kasashen waje su ma za su bude kofa ga kasar Sin. Ban da wannan kuma, manufar bude kofa ga kasashen waje da Sin take aiwatarwa ya kamata ta kasance mai amfani ga canja salon raya tattalin arzikin kasar da daidaita tsarin tattalin arzikin kasar, da sa kaimi ga aikin yin gyare-gyare da kirkiro da sabbin abubuwa, da haka ne, kasar Sin za ta kara daukar matakai don bude kofa ga kasashen waje.

"Sin za ta bude kofa ga kasashen waje a wasu sabbin fannoni, da kyautata halin da take ciki, wato za a bude kofa ga kasashen waje a yankunan da ba sa kusa da teku na, kazalika kuma, za a sa kaimi ga raya harkokin cinikin waje cikin daidaito, don tabbatar da yawan kayayyakin da za ta fitar, da fadada yawan kayayyakin da za ta shigar, don daidaita batun cinikin shige da fice da kasashen waje."

A yayin da kasar Sin ke bunkasa, masana'antun kasar Sin suna ta kara gudanar da harkokinsu a kasashen waje, sai dai masana'antun sun gamu da shingaye da wasu kasashen suka kafa. Game da wannan, Chen Deming ya bayyana cewa, dalilin da ya sa aka samu wannan matsala shi ne, sabo da wasu mambobin majalisar wakilai na kasashe masu wadata su ma suna daukar masana'antun kasar Sin ke gudanar da harkokinsu a ketare bisa tunani na yakin cacar baki. Ya ce, masana'antun Sin da suka je saka jari a kasashen waje, su samu karbuwa a kasashen duniya. Ya ce,"Alal misali, a Amurka inda kamfanoninmu suka samu matsala wajen saka jari inda kuma yanzu, muke da jarin da yawansa ya kai kudin Amurka sama da dala biliyan 10 a can, amma an amince da kashi 1 cikin 3 kawai na kudade da kamfanoninmu suka bayar don saka jari a can, hakika, wannan adadi ba shi da yawa, amma halin da ake ciki yana ta samu kyautatuwa, musamman ma yayin da na yi mu'amala da gwamnoni, da magadan birane da dama, da ma majalisun dokoki ta jihohi daban daban na kasar Amurka, na ga suna maraba da kamfanoninmu da suka je saka jari a kasarsu."

Haka kuma, Chen Deming ya ce, gwamnatin Sin ta bukaci kamfanonin Sin da suka je saka jari a kasashen waje da su bi dokokin wurin, da mutunta al'adunsu. A sa'i daya kuma, bayan da masana'antu suka samu moriya a wurin, ya bukace su da kawo alheri a wurin, kana kuma, gwamnatin kasar Sin za ta yi iyakacin kokari don tabbatar da hallacin hakkin kamfanonin Sin da suka je saka jari a kasashen waje.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China