in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana da fararen hula na kasar Nijeriya sun nuna kyakkyawan fata ga muhimman taruka biyu na kasar Sin
2013-03-04 11:25:48 cri






An kira taro na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na 12 na jama'ar kasar Sin, da zama na farko na majalisar wakilai na 12 na jama'ar kasar Sin a nan gaba kadan a nan birnin Beijing.

Wakilinmu ya yi hira da masanan Nijeriya masu binciken batutuwan kasar Sin da jama'ar kasar masu sha'awar bunkasuwar ta, wadanda dukkansu ke nuna kyakkyawar fata ga tarurukan biyu. Direktan sashin siyasa na jami'ar jihar Nassarawa dake Nijeriya, kuma masani dangane da batutuwan kasa da kasa farfesa Abdullahi Sallau Moddibo ya bayyana ra'ayin sa.

Babban taro karo na 18 na wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin da aka kira a watan Nuwamba na shekarar bara ya zabi sabbin shugabannin jam'iyyar. Kuma karo na farko ke nan da aka yi wadannan tarurukan biyu tun bayan kafuwar sabuwar kungiyar shugabancin jam'iyyar, haka kuma tarurukan 2 suna da muhimmanci sosai wajen mika mulkin kasar. A ganinsa, a gun tarurukan biyu da aka saba yi a ko wace shekara a kan tattauna wasu manyan batutuwan da suka shafi siyasa, da tattalin arziki, da bunkasuwar al'umma. Abin da aka sa gaba a wannan karo shi ne nanufofin tattalin arzikin da Sin za ta dauka nan gaba, da ma yadda Sin za ta ci gaba da raya dangantakar dake tsakaninta da kasashe masu tasowa.

Masanan kasar Nijeriya sun mai da hankali sosai kan yadda kasar Sin za ta tsayar da manufofi dangane da aikin diplomasiyya, musamman ma manufofi dake shafar kasashen Afrika. Masani mai bincike kan batun kasar Sin na jami'ar Abuja farfesa Mohammed Suleiman ya bayyana fatansa dangane da yadda za a raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka bisa manyan fannoni uku, wato bunkasuwar sha'anin noma, da samar da manyan kayayyaki more rayuwa, da kuma ba da horaswa ga masu fasaha.

Ban da haka, jama'ar kasar Nijeriya su ma suna mai da hankali sosai kan tarurukan biyu na kasar Sin. Daya daga cikin wadanda wakilinmu ya zanta da su mai suna Nuraddeen Ibrahim Adam, wanda yace ya taba ziyarci kasar Sin a shekarar 2011, inda ya gane ma idanunsa ci gaban da Sin da samu,ya bayyana kyakkyawan fatansa ga tarurukan biyu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China