in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin na kokarin ba da shawarwari kan gyaran tsarin rabon dukiyar al'umma
2013-03-13 18:28:00 cri






Bayan tsawon shekaru sama da 30 da kasar Sin ta shafe tana kokarin yin gyare-gyare a gida, tare da bude kofarta ga kasashen waje, yanzu kasar ta kasance ta biyu a duniya wajen ci gaban tattalin arziki, amma a waje guda, kasar ta fara fuskantar matsalar bambancin samun dukiya tsakanin sashen sana'o'i, da yankunan ta daban daban, matsalar da ta jawo hankalin mahalarta taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar a nan birnin Beijing, wadanda suka yi kokarin bayyana albarkacin bakinsu, tare da ba da shawarwarinsu a kan matsalar.
"A kowane wata, ban da kudin abinci, da kuma kudin biyan ruwa da lantarki, da iskar gas da kuma hayar gida, zan kuma kashe kudin da ya kai yuan dubu da dari uku zuwa hudu. Yanzu na tsufa, ga shi kuma ina fama da ciwon hawan jini, kowane wata, ina biyan kudin magani, don haka, kudin da ya rage ba shi da yawa."
A yanzu haka, bambancin albashi da kuma bambancin da ke tsakanin masu kudi da matalauta na zama matsalar da ke jawo hankalin jama'a.
Don haka, a watan da ya gabata, gwamnatin kasar Sin ta zartas da takardar ra'ayoyi kan inganta gyare-gyaren tsarin raba dukiya, inda kuma takardar ta fitar da dabaru, na rage bambancin da ke tsakanin matalauta da masu kudi, wato ta hanyar kara albashi ga wadanda ke samun kudin shiga kalilan, sa'an nan, a daidaita albashi ga wadanda ke samun kudin shiga da yawa, sa'an nan a kara yawan wadanda ke da matsakaicin kudin shiga.
A game da batun, dan majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kana shugaban cibiyar nazarin harkokin gyare-gyare da bunkasa ta kasar Sin, Chi Fulin yana ganin cewa, "kara kudin shigar mazauna birane da karkara" da aka gabatar, cikin shirin gyaran tsarin raba dukiyar al'umma, bai kamata ya haifar da karin gibi tsakanin matalauta da masu kudi ba, a maimakon haka, ya kamata ya taimaka ga kara yawan jama'ar da ke samun kudin shiga matsakaici. Don haka, ya gabatar da shawarar tabbatar da shiri da zai cimma burin rubanya yawan jama'ar da ke samun kudin shiga matsakaici nan da shekarar 2020, wato daga miliyan 300 zuwa kimanin miliyan 600. kamar yadda ya ce, "yanzu haka yawan jama'ar da ke samun kudin shiga matsakaita bai wuce kimanin kashi 23% ba, a halin da ake ciki, idan an rubanya kudin shiga ga kowane dan kasa, hakan zai iya kara fadada gibin da ke tsakanin matalauta da masu kudi ne kawai, don haka, abin da ya kamata mu sa lura shi ne, yadda za mu iya kara shigar da wadanda ke samun kudin shiga kalilan, cikin rukunin mutanen da ke samun kudin shiga matsakaici, wato a kara yawan jama'ar da ke samun kudin shiga matsakaici daga kashi 23%, zuwa kashi 40% nan da shekarar 2020."
Bayan da aka fitar da shirin gyara kan tsarin raba dukiyar al'umma, wasu sun bayyana damuwarsu kan cewa, idan an rubanya yawan kudin shigar al'umma, masu kudi za su kara samun kudin shiga fiye da saura, A game da haka, Mr.Jia Kang, dan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wanda kuma ya kasance shugaban cibiyar nazarin kimiyyar harkokin kudi a ma'aikatar kudi ta kasar Sin, ya ce, ya kamata a kyautata manufar haraji kan masu kudi. Misali ya kamata a mai da hankali a kan daidaita yawan kudin shigar ma'aikatan kamfanonin da ke yin babakere a wasu fannoni, ko kuma manyan darektoci na kamfanoni mallakar gwamnati, tare kuma da ma'aikatan hukumomin wasu sassa, wadanda suke samun kudin shiga mai armashi, kamar yadda ya fada, "A yayin da muke gudanar da gyare-gyare, ya kamata a yi la'akari da yadda wasu kamfanoni ke yin babakeren da bai dace ba, sa'an nan, a kara bayyana dokokin raba dukiyar al'umma a fili. A kuma kayyade albashin da bai dace ba, ga wasu manyan darektocin kamfanoni mallakar gwamnati."
Ban da wannan, matakin da aka gabatar cikin shirin gyaran tsarin rabon dukiyar al'umma, wato kara yawan kason da kamfanoni mallakar gwamnati suke mikawa ga gwamnati da kashi 5%, ya samu yabo daga wajen mahalarta taruka biyu, sai dai wasu na ganin cewa, yawan kason bai isa ba.
A game da kamfanoni mallakar al'ummar kasa kuwa, musamman wadanda ke yin babakere a wasu fannoni, mika wani kaso daga cikin ribar da suka ci, wata hanya ce ta inganta jin dadin al'umma, don haka, ya kamata su kara kason da suke bayarwa. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China