in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi kamfanonin Sin su yi kokarin magance hadari yayin da suke aiwatar da ayyukansu a kasashen waje
2013-03-07 18:23:18 cri






Kafin an fara manyan tarurruka biyu dake gudana a nan kasar Sin wato taron majalisar wakilan jama'ar kasar da ta bada shawarwa kan harkokin siyasa ta kasar, kamfanin Sany na kasar Sin ya gudanar da taron manema labaru, inda ya sanar da sakamakon da aka samu game da lamarin kai karar gwamnatin kasar Amurka a kotu da kamfanin Ralls dake karkashin jagorancin kamfanin Sany ya yi, kuma ya ce, kotun kasar Amurka ta riga ta karbi wannan kara da kamfnin Ralls kan shugaban kasar Barack Obama da kwamitin kula da harkokin yin amfani da jari daga kasashen waje. Wannan lamari ya sa batun kamfanonin Sin dake gudanar da ayyuka a kasashen waje ya zama wani muhimmin batu a gun taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a wannan karo.

A ranar bude taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12, ministan kula da harkokin cinikayya na kasar Sin Chen Deming ya yi jawabi game da lamarin kai karar gwamnatin kasar Amurka da kamfanin Sany na kasar Sin ya yi. Chen Deming ya bayyana cewa, yanzu ana yin bincike kan lamarin, kuma za a samar da taimako da bada kariya ga kamfanin Sin bisa doka. Ya ce,"Wannan lamari yana shafar dangantakar dake tsakanin wani kamfanin kasar Sin da gwamnatin wata kasar waje. Gwamnatin kasar Sin tana sa lura da yin bincike kan lamarin bisa doka. Bisa ka'idojin hukumar cinikin duniya wato WTO, ma'aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin tana da ikon bada kariya ga kamfanonin kasar idan suka samu hasara. Kana ma'aikatar tana da sashen yin ciniki cikin daidaici da kuma sashen bincike kan hasarorin da kamfanoni suka samu, bayan da kamfanoni suka gabatar da bukatunsu gare su, za su samar da taimako ga kamfanonin."

Zargin gwamnatin kasar Amurka da kamfanin Sany ya yi ya faru ne dalilin wani umurnin da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bada a watan Satumba na shekarar bara, inda ya bukaci a dakatar da ayyukan samar da wutar lantarki ta hanyar iska da kamfanin Ralls da kamfanin Sany ke yi a jihar Oregon ta kasar Amurka bisa dalilin kawo barazana ga tsaron kasar. Wannan ba karo na farko ba ne da kamfanin Sin ya samu hasara bisa dalilin siyasa. Don haka, batun magance hadari ya zama abu mai muhimmanci ga kamfanonin Sin dake gudanar da ayyukansu a kasashen waje.

A shekarun nan, kamfanonin Sin sun kara gudanar da ayyukansu a kasashen waje, kuma abkuwar rikicin hada-hadar kudi na duniya ba ta sassauta saurin ci gabansu ba. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan jarin da kasar Sin ta zuba ba na hada-hadar kudi ba ya kara daga dala biliyan 24.8 a shekarar 2007 zuwa dala biliyan 77.2 a shekarar 2012, yawansu ya karu da kashi 25.5 cikin kashi dari a kaddarance a kowace shekara. Don haka, an kara samun hadari ne kan hadin gwiwa da zuba jari da kamfanonin Sin suka yi a kasashen waje.

Game da wannan batu, dan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a wannan karo kuma shugaban kamfanin TCL na kasar Sin Li Dongsheng ya nuna cewa, kamata ya yi kamfanonin Sin su yi bincike kafin gudanar da ayyuka a kasashen waje. Ya ce,"Ina ganin cewa, da farko ya kamata kamfanonin Sin su tabbatar da burinsu da yadda za su yi kafin su fara aiki a kasashen waje. Na biyu kuwa, tilas ne kamfanonin Sin su shirya sosai, domin za su fuskanci kalubale da dama a kasashen waje."

'Yar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin kuma mataimakiyar shugaban kamfanin Midea Yuan Liqun ta bayyana cewa, bayan da aka aiwatar da manufar bude kofa da yin kwaskwarima a kasar Sin, an samar da dama mai yawa ga kamfanonin Sin a sakamakon bunkasuwar tattalin arzikin kasar cikin sauri. Don haka, kamfanoni da dama sun rike wannan dama, sun fara gudanar da ayyukansu a kasashen waje ta hanyar zuba jari da yin kirkire-kirkiren kayayyakinsu, ta haka sun daga karfinsu sosai.

Yuan Liqun ta nuna cewa, domin yanayin tattalin arzikin duniya ba ya da kyau a yanzu, kamata ya yi kamfanonin kasar Sin su yi kokarin magance hadari yayin da suke gudanar da ayyukansu a kasashen waje. Ta ce,"A shekaru biyu da suka gabata, an samu sauyin yanayin tattalin arzikin duniya. A hakika dai, rikicin hada-hadar kudi na duniya ciki har da matsalar yawaitar bashi a nahiyar Turai yana ci gaba da kawo illa ga tattalin arzikin duniya, ba a warware wasu manyan matsalolin da aka samu a sakamakon rikicin ba. Don haka, kamfanoni na fuskantar sabbin dama tare da sabbin kalubale a duniya."

A shawarar da Yuan Liqun ta bayar a gun taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a wannan karo, ta yi kira ga gwamnatin kasar da ta kara nuna goyon baya ga kamfanonin kasar Sin wajen gudanar da ayyukansu a kasashen waje. Tana fatan gwamnatin kasar da kamfanonin kasar su yi kokari tare don cimma burin bude kofa yadda ya kamata. Ta ce,"Ana fatan gwamnatin kasar Sin za ta kara nuna goyon baya ga kamfanonin kasar ta sabbin hanyoyi. Kana kamata ya yi kamfanoni su kara yin kwaskwarima da yin kirkiro a fannonin fasahohi, kudi, haraji, horar da ma'aikata da dai sauransu." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China