in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a fara taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin
2013-03-04 17:55:45 cri






Gobe Talata 5 ga wata ne, za a fara taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin. A ranar Litinin 4 ga wata a nan birnin Beijing ne, aka gudanar da taron manema labarai karo na farko dangane da taron, inda kakakin taron kana babbar jami'ar diplomasiyya ta kasar ta amsa tambayoyin daruruwan manema labarai na gida da waje da ke halartar taron kan abubuwan da ke daukar hankalin al'umma, wadanda suka hada da yaki da cin hanci da rashawa, kiyaye muhalli, kasafin kudin tsaron kasa da makamantansu.

Madam Fu Ying ta taba zama mataimakiyar ministan harkokin waje na kasar Sin, kana ita ce mace ta farko da ke magana da yawun taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin. Da farko, Madam Fu ta yi bayani a kan ajandar taron da za a fara, inda ta ce, "za a fara zama na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12 a gobe Talata 5 ga wata da safe, kuma za a rufe taron a ranar 17 ga wata da safe, wato ke nan za a dauki tsawon kwanaki 12 da rabi ana taron. Bayan da aka rufe taron kuma, sabon firaministan kasar Sin da aka zaba zai gana da manema labarai na gida da na waje, don amsa tambayoyin da ke daukar hankalin duniya."

An zabi wakilan jama'a mahalarta taron ne bisa dokar zabe da aka yiwa gyara a shekarar 2010, don haka, wakilan da aka zaba sun jawo hankalin al'umma. Madam Fu Ying ta bayyana cewa, "Misali, idan an kwatanta sabbin wakilai da kuma tsoffin wakilai, za a ga cewa, wakilan ma'aikata da na manoma sun karu da 155, wato ke nan kasonsu ya karu da kimanin kashi 5 cikin 100, sa'an nan, yawan wakilan manoma 'yan cin rani ya kai 31, ana fatan sauraron ra'ayoyin da za su bayyana a madadin wadanda suke wakilta. A sa'i daya kuma, an rage wakilan mahukunta da kimanin kashi 7 cikin 100."

A gun taron, manema labarai a cikin sa'a guda sun gabatar da tambayoyi 9 ga kakakin, wadanda suka shafi yakar cin hanci da rashawa, kiyaye muhalli, manufar diplomasiyya da kuma gyaran tsarin siyasa da sauransu.

Wani dan jarida na kasar Japan ya yi tambayar cewa, ko kasar Sin za ta kara nuna fin karfi a harkokinta na diplomasiyya? A game da tambayar, madam Fu Ying ta ce, a yayin da kasar Sin ke ta bunkasa, tana ta jawo hankalin duniya. Sai dai wasu ba su fahimci hakan ba, kuma bisa ga yadda suka gano daga tarihi cikin shekaru 500 da suka wuce, su kan yanke hukuncin cewa, idan wata kasa ta bunkasa, ta kan nuna fin karfi, don haka kasar Sin ita ma za ta yi kamar haka. Dangane da wannan, madam Fu Ying ta ce, "Da farko, idan mun yi nazari bisa manufa, kasar Sin tana bin manufar diplomasiyya ta kiyaye 'yancin kanta da zaman lafiya a duniya. A sa'i daya, za mu yi kokarin kiyaye mulkin kanmu, sannan kuma, muna kokarin kiyaye zaman lafiya a duniya, wannan tsayayyiyar manufa ce da ba mu taba sauyawa ba cikin shekaru 30 da suka wuce. Amma yayin da matsala ta bullo, a yayin da muke fuskantar matsalar da ta shafi ikon kasa na mallakar yankinta, da kuma lokacin da muke fuskantar kalubalen da wasu kasashe suka haddasa mana, me za mu yi? To, dole ne mu fuskanci matsalar kuma mu dauki matakai da suka dace na warware ta. Ina ganin wannan shi ma muhimmin sako ne da muka aika ga shiyyar na kiyaye zaman lafiya a shiyyar."

Duk da cewa, kasar Sin tana tsayawa kan bin hanyar samun ci gaba cikin lumana, amma a yayin da yanayin duniya ke sauyawa, an yi ta ce-ce-ku-ce kan sauya manufarta ta diplomasiyya da na tsaron kasa da kasar Sin za ta yi. A game da batun, Madam Fu Ying ta jaddada cewa, "babbar kasa kamar kasar Sin, idan ta kasa kiyaye tsaron kanta, wannan ba zai kasance labari mai dadi ga duniya ba. Mun ji zafin yadda wasu suka ci zarafinmu a yayin da ba mu da karfin tsaron kanmu a cikin shekarun da suka wuce, tarihin da ba za mu taba mantawa da shi ba. Don haka, muna bukatar karfin da ya dace na tsaron kanmu, kuma ingantuwar harkokin tsaron kasar Sin ma za ta taimaka ga kiyaye kwanciyar hankali a shiyyar da kuma zaman lafiya a duniya baki daya. Mun dade muna bin manufar tsaron kasa ta kiyaye zaman lafiya da kuma kare kanmu, kuma muna inganta harkokin tsaron kasa ne domin kiyaye zaman lafiya da tsaron kanmu, ba domin barazana ga wata kasa ba."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China