in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na nacewa manufar tsaron kasa bisa kyakkyawar manufa
2013-03-12 17:11:25 cri






A yanzu ana ci gaba da taron shekara-shekara na babbar hukumar madafun iko ta kasar Sin a nan birnin Beijing, an kuma kawo karshen taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa. Yayin taron, an gabatar da kasafin kudin da Sin za ta kashe a bangare aikin soja, matakin da ya jawo hankalin kasa da kasa.

Wani abun lura ma shi ne yadda aka kambama matsayin kasar ta Sin, har ta kai wasu na ganin kasar zata iya kawo barazana ga wasu kasashen duniya, saboda sabbin makaman data kera, da mawuyacin halin da take ciki dangane da batun tsaro a kewayenta. Game da wadannan jita-jita da aka yi, 'yan majalisun guda biyu masu kula da aikin soja, sun yi hira da wakilinmu.

Sin ta kara yawan kasafin kudi dangane da aikin soja bisa bukatun tsaron kasa, wanda hakan ya dace da bunkasuwar tattalin arzikinta, hakan kuma mataki ne da ba zai kawo barazana ga kasashe dake makwabtaka da ita ba. Sin na nacewa ga manufar tsaron kasa ta kare kai, har ila yau, batun tsaro da kasashen dake kewayenta suke fuskanta ba zai haifar da rikici ba. Ko da yake, Sin ta kara kudin da za ta kashe a wannan fanni, amma yawansu bai kai wanda wasu kasashe, ciki hadda Amurka, da Birtaniya, da Faransa da sauransu ke kashewa ba.

Shugaban rukunin masana dake bada bayyanai kan aikin tsaron kasar Sin, kuma dan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, kuma mai bincike na kwalejin binciken kimiyar aikin soja na kasar ta Sin Chen Zhou na ganin cewa:

"Sin ta kara kudin tsaron kasa ne bisa bukatun da ake da su a wannan fanni a 'yan shekarun nan, wanda kuma ya dace da bunkasuwar tattalin arzikin kasar. Ya zuwa yanzu, Sin ta samar da daidaito wajen kara kudin da za ta kashe dangane da aikin soja yadda ya kamata, kuma sha'anin tsaron kasa zai dace da bukatun jama'a a wannan fanni, tare da bunkasuwar tattalin arziki."

A yayin taruka biyu, ban da kasafin kudin tsaron kasar, ana mai da hankali sosai kan canjin da sojojin kasar suke fuskanta tun daga shekara bara. A cikin karshen shekarar 2012, babban sakatare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, a karo na farko ya gabatar da ra'ayin inganta sojin kasar bisa jigon "Samun nasara cikin yaki, da gudanar da harkokin soja bisa doka".

Game da wannan batu, dan majalisar wakilan jama'a daga rundunar dake sarrafa makamai masu linzami, kuma shugaban birged ta biyu dake sarrafa makaman igwa Tan Weihong ya ce:

"Yanzu, muna mai da hankali sosai kan horar da sojojinmu don tinkarar duk wasu yake-yake. Kuma muna kara inganta horo da za mu bayar, ta yadda sojojinmu za su iya warware wasu matsaloli, a lokacin barkewar yaki."

Ban da haka, an kyautata ka'idar da Sin take bi a fannin soja saboda wasu matsalolin da kasar ke fuskanta, wadanda kuma suke kara tsananata, ciki hadda batun tsibirin Diaoyu da tekun Nan Hai. Amma, wasu kafofin yada labaru sun yi hasashe bisa kuskure, inda suke cewa, Sin na shiri shiga wani yaki ne.

Sin na matukar musanta haka, wakilai a fanni soja sun bayyana cewa, cimma nasara yayin yaki, bukata ce mai tushe ga ayyukan soja. Dan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, kuma tsohon direktan ofishin harkokin waje dangane da tsaron kasa Qian Lihua ya ce:

"Babu bukatar damuwa da halin da Sin ke ciki dangane da yanayin tsaro a kewayenta. Kamata ya yi mu fuskanci wannan hali yadda ya kamata. A matsayi na na soja, ina ganin cewa, matsalar tsaron da Sin take fuskanta, ko kadan, ba za ta haifar da rikici, balle yaki ba."

Babban batun da Sin take fuskanta dangane da yankin kasa shi ne, tabbatar da shatin iyakar sararin teku. A cikin rahoton da aka bayar cikin taro karo na 18 na wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin an gabatar da cewa, ya kamata, Sin za ta kara karfinta a teku, kuma rahoton ayyukan gwamnatin kasar Sin da aka bayar a wannan shekara, ya jaddada wajibcin kiyaye ikon kasar a kan teku. A shekarar bara, Sin ta fara amfani da babban jirgin ruwan yaki mai saukar jiragen saman yaki, ban da haka, sojin teku sun gudanar da horo a tekun Pacific sau da dama, tare kuma da yin sintiri a kewayen tsibirin Diaoyu.

Game da bunkasuwar sojin teku, dan majalisar wakilan jama'a, kuma mataimakin kwamandan rukunin jiragen ruwan yaki a tekun Dong Hai, Sun Laishen ya nuna cewa, Sin ba kawai na da yankin kasa da fadinsa ya kai muraba'in kilomita miliyan 9.6 ba ne, har ma tana da sararin tekun da fadinsa ya kai muraba'in kilomita miliyan 3. Don haka sojin teku na da imanin kiyaye sararin tekun kasar, tare da tinkarar duk wani kalubale a kan teku. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China