in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta ci gaba da sanya moriyar jama'a a gaban kome yayin da take kokarin yin gyare-gyare
2013-03-05 16:39:08 cri






An bude babban taron zaman farko na sabuwar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a yau Talata 5 ga wata a nan birnin Beijing. A cikin rahoton da ya gabatar wa taron game da ayyukan gwamnatin kasar, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya jaddada cewa, yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, babban tushe ne na neman bunkasuwar kasar Sin, sabo da haka kamata ya yi a kara inganta wannan sashe.

"Yanzu kasar Sin na cikin yanayi mai tsanani a fannin yin gyare-gyare a gida, dole ne mu kara tunaninmu don inganta gyare-gyare a fannonin tattalin arziki, da siyasa, da al'adu da zaman al'umma da dai sauransu, ta haka ne za a karfafa nasarar aikin yin gyare-gyaren."

A madadin gwamnatin mai ci, a kuma gaban sabbin wakilai kusan 3000, mista Wen Jiabao ya gabatar da rahoton ayyuka na karshe a cikin wa'adin aikinsa, a babban dakin taro na jama'ar kasar Sin, inda aka takaita ayyukan da gwamnatin ta gudanar a cikin shekaru 5 da suka wuce, tare kuma da gabatar da abubuwan da suka wajaba wajen samar da ci gaban tattalin arziki da kyautatuwar zaman rayuwar al'umma, da babban burin da ake fatan cimmawa, da kuma babbar manufar tattalin arziki. Kazalika an ba da shawarwari kan yadda sabuwar gwamnatin za ta gudanar da ayyukanta.

A dakin taron, wakilai mahalarta na mayar da hankali sosai kan nazartar burin sabuwar gwamnati ta fuskar gudanar da ayyukanta.

Wasu al'umma da suka bayyana ra'ayoyinsu a sassan birnin Beijing don gane da taron ma sun nuna sabon fata game da zaman rayuwarsu a nan gaba.

"Ina cikin yanayi mai kyau wajen samun abinci, da harkokin wasanni, ina iya samun kulawa idan na tsufa, lallai zaman rayuwata yana matsayi mai kyau. Hakika na gamsu da yanayin da nake ciki, ko da yake zai fi kyau idan na kara samun wadata."

"A ganina, zaman rayuwata na kara samun kyautatuwa, ina fatan za a kara kyautata manufofi, ta yadda zan iya sayen gida na kaina."

Abubuwan da jama'a ke bukata, buri ne da kasarsu za ta yi kokarin cimmawa. Bayan shekaru sama da 30 da suka wuce, lokacin da aka yi gyare-gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje, ta yaya za a sanya dukkanin jama'ar kasar Sin cikin gajiyar nasarorin da aka samu a fannin bunkasuwa, wannan ya kasance muhimmin aiki ne ga gwamnatin. Wen Jiabao ya yi bayani a cikin rahoton yana mai cewa,

"Mun mai da samar da aikin yi a gaban komai yayin da muke kokarin ba da tabbaci da kyautata zaman rayuwar jama'a. A cikin shekaru biyar da suka wuce, mun zuba kudin musamman kimanin RMB biliyan 197.3, yawan daliban da suka samu aikin yi bayan da suka gama karatu a jami'o'i ya kai miliyan 28, kuma an shimfida tsarin inshora game da aikin kula da tsofaffi ga jama'ar birane da kauyuka dake dukkanin fadin wannan kasa."

A cikin wadannan shekarun biyar, kasar Sin ta fuskanci kalubaloli sakamakon matsalar hada-hadar kudi ta duniya, da bala'un da suka afkawa wurare masu tsanani. Amma, duk da haka yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasar wato GDP ya karu zuwa matsayi na biyu a dukkanin duniya.

Mista Wen ya amince da cewa, har yanzu ana fuskantar wasu matsaloli, ciki hada da rashin daidaito wajen samun bunkasuwa, da rashin samun dauwamammen ci gaba, matsalolin da ya ce kamata ya yi a warware su ta hanyar yin gyare-gyare.

Kan maganar ayyukan sabuwar gwamnatin, mista Wen ya ba da shawarar cewa,

"Kamata ya yi a kara kyautata tsarin tattalin arziki na kasuwanci irin na gurguzu, don kafa wani ginshiki mai kyau, ga samun daidaito tsakanin sassan tsarin mallakar tattalin arziki daban daban. Mun riga mun kaddamar da ka'idoji game da zurfafa yin gyare-gyare kan tsarin raba kudin shiga. Kamata ya yi a tsara hakikanin manufofi, don sanya duk jama'ar kasa cin gajiyar nasarorin da aka samu sakamakon bunkasuwa. Bugu da kari, akwai bukatar tsayawa tsayin daka kan adawa da cin hanci da rashawa, da kuma bin babbar manufar bude kofa ga kasashen waje." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China