in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na mai da hankali kan ingancin abinci
2013-03-15 16:53:49 cri






Ranar 15 ga watan Maris rana ce ta kare hakkin masu sayen kayayyaki ta kasa da kasa, don haka, ingancin abinci ya sake zama wani muhimmin batu dake janyo hankalin al'ummar kasar Sin, wanda kuma ya kasance wani babban batu da wakilan jama'ar kasar, wadanda ke halartar taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a nan birnin Beijing, suka mai da hankali a kai.

Mista Chen Xuyuan, daya daga cikin wakilan jama'ar kasar Sin, wanda kuma babban darekta ne na wani kamfani mai kula da tashar jiragen ruwa a yayin taron majalisar wakilan jama'a dake gudana, ya gabatar da shawarar cewa, a yi wa dokar tabbatar da ingancin abinci kwaskwarima duk da cewa aikinsa bai shafi harkar samar da abinci ba.

'Dalilin da ya sa na gabatar da wannan shawara shi ne, da farko, jama'ar dake zama kusa da ni, da abokan aikina da yawa suna fatan in yi kira ga gwamnati da al'ummar kasarmu domin su dora muhimmanci kan batun tabbatar da ingancin abinci. Na biyu shi ne, ni ma na fahimci cewa akwai matsaloli da dama da suka shafi ingancin abinci, wadanda suka sabawa matsayin kasarmu a duniya, wadanda kuma su kan sanya rashin jin dadi tsakanin jama'a.'

Shi ma a nasa bangaren, Mista Ge Junjie, mataimakin babban darektan kamfanin samar da madara mai suna Bright Dairy, kuma daya daga cikin wakilan jama'ar kasar Sin, ya fahimci mummunan sakamako da matsalar ingancin abinci ka iya haifarwa. Bisa la'akari da aikinsa na sarrafa abinci, ya ce,

'Bisa matsayina na wakilin jama'a wanda ke kula da aikin samar da abinci,ina ganin aikin tabbatar da ingancin abinci yana da muhimmanci kwarai da gaske. Idan mun kasa daidaita matsaloli dake wannan fanni, za su iya kawo matsala ga kokarinmu na tabbatar da jituwa a zaman al'umma da kuma kwanciyar hankali. Don haka, mun dauki aikin tabbatar da ingancin abinci a matsayin wani muhimmin bangare a yunkurin wanzar da sulhu tsakanin al'ummar kasar. A shekarun baya, na dade ina jin cewa akwai matsaloli da dama cikin tsarin sa ido sakamakon yadda sassan gwamnati da dama suke sanya hannu a ciki a sa'i guda, da ma tsarin da muke bi wajen gudanar da aikin, don haka nake ta kokarin mika shawarwari don kyautata tsarin sa ido kan ingancin abinci.'

Maganar Mista Ge tayi daidai da ra'ayin wasu kwararru, wadanda ke nuni da cewa, babban dalilin da ya sa ake samun matsaloli da yawa a fannin tabbatar da ingancin abinci a kasar Sin, shi ne saboda yadda ake rarraba ikon sa ido ga sassan gwamnati daban daban. Amma ana sa ran ganin cewa za a samu damar kawar da wannan matsala sakamakon yadda ba da jimawa ba za a kafa wata babbar hukumar sa ido kan ingancin abinci da magunguna ta kasar Sin, wadda za ta hada ikon da aka rarraba zuwa waje daya.

Haka zalika, Mista Zhong Nanshan, wani babban masani a kasar Sin, kuma daya daga cikin wakilan jama'ar kasar, ya ce da ma tsarin da gwamnatin kasar take bi wajen sa ido kan ingancin abinci yana da aibi, inda hakan ke hana a gudanar da aikin sa ido yadda ya kamata, kana har yanzu babu matakan da aka bayyana a fili don hukunta masu laifi ta wannan fanni. Amma shi ma yana sa ran ganin cewa babbar hukumar sa ido da za a kafa a wannan karo za ta shawo kan matsalar da ake fuskanta. Ya ce,

'A ganina alkiblar da aka dosa ta yi daidai, kuma na yarda da kwaskwarimar da ake gudanarwa. To amma wane sakamako ne za a iya samu daga kwaskwarimar ya dogaro ne kan matakan da za a dauka, game da yadda hukumar za ta aiwatar da aikinta, wato ke nan ko za ta iya samun cikakken ikon sa ido, da yadda za ta raba ayyuka ga sassanta daban daban, da ma wani abu mai muhimmanci wato kamar tsarin sa ido. Tsarin sa ido shi ne babban batu da ya kamata majalisar wakilan jama'a ta lura da shi.'

Wasu jami'ai masu kula da aikin sa ido kan ingancin abinci su ma sun yi nuni da cewa, garambawul da ke gudana a wannan karo zai iya daidaita matsalolin da ake fuskanta sakamakon kasancewar tsarin raba ikon sa ido tsakanin hukumomi daban daban, don haka zai kawo ingancin tsarin sa ido da kuma irin fasaha da ake amfani da ita don gudanar da aikin sa ido, ta yadda za a iya tabbatar da ingancin abinci da karfafa wa jama'a kwarin gwiwa a wannan fanni.

Ban da haka, wasu kwararru na ganin cewa, matakan da suka shafi kara kwarjinin gwamnati, da kuma baiwa jama'a bayanai a kan lokaci, za su taimaka matuka, a kokarin da ake yi na tabbatar da ingancin abinci.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China