in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta dauki matakai da dama don tabbatar da samun isashen hatsi
2014-03-12 17:56:12 cri

Ya zuwa shekara ta 2013, kasar Sin ta samu karuwar yawan hatsi a tsahon shekaru 10 a jere. Sai dai sakamakon karuwar habakar birane da garuruwa, gonakan noma na ragu, kuma manoma da yawa suna kaura zuwa birane da manyan garuruwa, matakin da ya sanya batun yaya za a tabbatar da samun isashen hatsi ke jawo hankulan jama'a matuka.

Bisa labarin da muka samo daga tarurukan shekara-shekara, na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, an ce, a halin yanzu kasar Sin tana daukar matakai da dama, don tabbatar da samun isashen hatsi yadda ya kamata.

Baya ga yadda taron kwamitin tsakiya na JKS kan tattalin arziki, da aka shirya a karshen shekarar bara, da takardar tabbatar da kuduri da kwamitin tsakiya na JKS a farkon shekarar bana, suka mayar da aikin tabbatar da samun isashen hatsi a wani matsayi mai muhimmanci, a hannu guda, rahoton aikin da firaministan Sin Mista Li Keqiang ya gabatar yayin bude taron shekara-shekara, na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a 'yan kwanakin baya, ya sake bayyanawa a fili cewa, gwamnatin za ta mayar da maganar habaka samar da hatsi bisa karfin kasa kan gaba, da tabbatar da kwarewar kasar wajen samar da isashen abinci ga Sinawa biliyan 1.3 bisa karfin kasar a matsayin babban aiki mai muhimmanci da gwamnati za ta sanya a gaba a shekarar nan ta 2014.

A ganin ministan aikin gona Mista Han Changfu, a matsayin ta na kasa da ke da jama'a masu yawan gaske, ya zama dole kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan tabbatar da samun isashen hatsi bisa karfin kan ta. Ya ce,

'Yawan cinikayyar hatsi a duniya baki daya ya kai kilogram biliyan 300, wanda ya yi daidai da rabin hatsin da muke samu. Shinkafa kuwa a matsayinta na abincin farko da muka fi ci, ana cinikayyarta kusan kilogram biliyan 35 a duk duniya, wanda ya yi daidai da rubu'in shinkafar da muke ci, cinikayyar kuma da ba ta shafe mu kawai ba, tuni muka fahimci hakan.'

A halin da kasar Sin take ciki, idan tana son tabbatar da samun isashen hatsi bisa karfin kanta, dole ne ta fuskanci kalubaloli da dama. A yunkurin habaka birane da garuruwa, gonakan noma sun ragu, manoma da dama sun kaura zuwa birane, kuma ba a samun riba mai yawa daga noman hatsi, lallai kasar Sin tana bukatar daidaita wadannan matsaloli. Daga wadannan matsaloli akwai batun yaya za a daga himmar manoma kan noman hatsi.

Wani matashi mai suna Xiaocao dan shekaru 23 da haihuwa, wanda ya zo daga kauyen Heze na lardin Shandong na kasar Sin, ya riga ya shafe shekara daya ko fiye yana sai da kayayyakin lambu a wata kasuwar da ke a nan birnin Beijing. sakamakon yadda ya bar aikin gona a kauyensa, ya bayar da gonakansa a hannun wani mutum don ya yi amfani da su. Ya ce

'Yawancin manoma a kauyenmu suna cin rani a birane, kakata da uwata ne kawai suna gida, akwai gonakai da yawa da bama iya nomansu.'

'Kudin shiga da ake samu a aikin noma a shekara daya, bai kai kudin shiga da ake samu daga cin rani a birni cikin wata guda ba.'

Matasa irinsu Xiaocao suna da yawa. Bayan da matasa 'yan kwadago da yawa suka kaura daga kauyuka zuwa birane, wurare da yawa na kasar Sin ba sa samun isassun manoma da ke da karfin gudanar da aikin noma. Game da haka, 'dan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kuma babban masanin tattalin arziki na ma'aikatar aikin gona ta kasar Sin Mista Qian Keming ya ce,

'A halin yanzu, kusan kowane iyali na manoma yana da wani matashi da ke shiga birane samun aikin yi, kuma ribar da ake samu daga hatsin da ake noma ta ragu, da akwai wasu gonakai da ba a iya nomawa a kauyuka, ba wanda ya san wanda zai iya noma su a nan gaba.'

'Dan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kuma darektan ofishin kula da harkokin kauyuka na kwamitin tsakiya na JKS Mista Chen Xiwen ya bayyana cewa, kara kudin shiga ga manoma, da inganta himmarsu wajen noma kadai, zai iya tabbatar da samun isashen hatsi yadda ya kamata, da samar da tarin amfanin gona ga kasuwannin kasar Sin. Ya ce,

'Idan ana iya samun riba mai yawa, tabbas ne za a kara nuna himmar gudanar da noman hatsi. Komai wuyar aiki, idan akwai riba babba cikin sa, to kuwa tabbas za a yi shi.'

Rahoton aiki da gwamnatin kasar Sin ta gabatar ya yi nuni da cewa cewa, duk da matsalar da gwamnati take samu ta fannin karancin kudi, za a tabbatar da kara zuba jari kan aikin gona a maimakon a rage su. Ministan aikin gonan kasar Sin Mista Han Changfu shi ma ya yi nuni da cewa, a nan gaba, kasar Sin za ta bayar da kudin rangwame a sabon karo, ga manoman da ke noman hatsi bisa babban mataki.

'A ganina, ya kamata gwamnati ta kara bayar da kudin rangwame ga aikin gona. Kasashen Turai da Amurka su kan bayar da kudin rangwame kashi 40 bisa dari ga manoma, amma kudin da muke baiwa manoma kai tsaye bai wuce kashi 3 bisa dari ba kacal. Sabo da haka muna iya cewa, gwamnati za kara samar da kudin rangwame ga aikin gona.' (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China