in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da yin kwaskwarima kan hukumomin majalisar gudanarwa
2013-03-01 16:04:18 cri






Jam'iyyar dake jan ragamar mulkin kasar Sin wato jam'iyyar kwaminis ta Sin ta bayar da wata sanarwa a ran 28 ga watan Fabrairu dangane da taron daukacin hukumomin kwamitin tsakiyar kasar Sin, wadda ta nuna cewa, kwamitin tsakiyar jam'iyyar JKS ya zartas da shirin yi wa hukumomin kasar kwaskwarima, tare kuma da ba da shawara ga majalisar gudanarwa da ta mika wannan shiri ga taro karo na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12, da za a yi a ran biyar ga wannan wata. Sanarwar har wa yau ta bayyana cewa, ya kamata, Sin ta dage kan matsayin gudanar da ayyukan gwamnati bisa moriyar jama'a, tare kuma da hada ba da hidima da sa ido waje guda.

Cikakken zama na biyu na kwamitin tsakiya na jam'iyyar JKS, karo na 18 ya ba da wata sanarwa cewa, ya kamata, a ci gaba da yin kwaskwarima kan hukumomin gwamnati, kyautata tsare-tsaren gwamnati da kuma karfafa karfin gwamnati bisa tushen juya ayyukan gwamnatin. Wanda ya kasance karo na bakwai da aka yi wa gwamnatin kwaskwarima.

Farfesa sashin binciken manufar sa ido don kula da kayan al'umma na kwalejin koyar da ilmin gudanar da ayyukan gwamnati na kasar Sin Zhu Lijia yayi nuni da cewa, za a yi kwaskwarima a wannan karo bisa koyi da abinda aka samu daga wanda aka taba yi a shekarar 2008

Ban da haka, a wannan karo za a mai da hankali sosai kan juya ayyukan da gwamnati za ta yi nan gaba, wato mai da hankali kan kyautata zaman rayuwar jama'a, kara ba da hidima ga al'umma da kuma kyautata hukumomin ba da hidima, ta yadda za a kauracewar yin aiki marasa amfani ko rashin daukar matakai idan bukatar hakan ta taso, saboda ganin cewa za a canja ayyukan gwamnati. Mr Zhu ya ce:

"An samu ci gaba mai kyau cikin kwaskwarima da aka yi a shekarar 2008 wanda ya zamo jigon canja ayyukan gwamnati. Kuma an kafa wani tsari mai amfani wanda ya dace da tsarin tattalin arzikin kasuwannin kasar Sin irin na gurguzu da bunkasuwar al'ummar Sinawa. Duk da haka, ana fuskantar wasu kalubale, musamman ma wajen daidaita harkokin hukomomi daban-daban da kuma dangantakar dake tsakanin sassa daban-daban. Ban da haka, akwai sauran ayyukan da suka wajaba a yi kwaskwarima kan su. Kwaskwarima da za a yi a wannan karo, ya kamata, su warware wadannan batutuwa tare kuma da kafa wata gwamnati da zata iya ba da hidima ga jama'a dake karkashin jagorancin al'umma."

Muna iya gani daga sanarwar da cikakken zama na biyu na kwamitin tsakiya na jam'iyyar JKS a karo na 18 ya bayar cewa, shirin yi wa hukumomin majalisar gudanarwa kwaskwarima ya kayyade ikon gwamnati, wato baiwa hukumomi daban-daban iznin gudanar da ayyukansu bisa karfin kansu, a maimakon haka, gwamnati ta dora muhimmanci sosai kan wasu manyan ayyuka, kamar kara karfin kafa manufofi masu tushe da gudanar da ayyukanta bisa doka. Mr Zhu ya bayyana cewa:

"Ya kamata, gwamnatin tsakiya ta baiwa kananan hukumomi iznin gudanar da ayyuka bisa karfin kansu, da kuma sa kaimi ga raya kungiyoyi masu zaman kansu. Yanzu, kungiyoyi masu zaman kansu ba su da karfin gudanar da ayyukan da gwamnati za ta dora musu. Ya kamata, mu yi kokarin juyawa da tabbatar da ayyukan gwamnatin saboda ganin wajibcin bunkasuwar al'umma mai inganci da kyautata zaman rayuwar jama'a, raya al'umma wacce ta dace da zamani tare da raya kasar Sin yadda ya kamata."

Za a fuskanci hadewar hukumomi yayin da ake yin kwaskwarima. A shekarar 2008, an kyautata hukumomi 15, inda kuma aka kafa sabbin hukumomi, ciki hadda hukuma mai kula da masana'antu da sadarwa, hukuma mai kula da zirga-zirga da sufurin kayayyaki, hukuma mai kula da kwadago da ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a ta kasar Sin, hukumar kiyaye muhalli, da kuma hukuma mai kula da gidaje da raya birane da kyauyuka.

A wannan karo, za a mai da hankali sosai kan ko za a kafa wata hukuma dake ba da tabbaci ga ingancin abinci ko a'a, da kuma ko za a hada sashin jiragen kasa da hukumar zirga-zirga da sufurin kayayyaki ko a'a, tare da mai da hankali sosai kan yadda za a warware matsalar kasa samun tikitin ta jirgin kasa a bikin sabuwar shekarar kasar Sin bisa kalandar gargajiya.

A ganin malam Zhu, hukumomi daban-daban na kasar su tabbatar da sa ido kan ayyukansu yadda ya kamata,sannan yaki da cin hanci da karbar rashawa na da muhimmanci sosai cikin kwaskwarimar da za yi. Ya kamata, a mai da hankali sosai kan wadannan fannoni maimakon yin hadewar hukumomi. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China