in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi a kyautata tsare-tsare da farko yayin da ake kokarin yaki da cin hanci da rashawa
2013-03-11 17:16:57 cri






A yanzu haka ake yin taruruka biyu na hukumar iko ta koli ta kasar Sin, da ta ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar a nan birnin Beijing.

Bisa binciken da kafofin watsa labaru suka yi game da batutuwan da suke jawo hankalin jama'a a, an nuna cewa, a shekarun baya-bayan nan, yaki da cin hanci da rashawa yana kan matsayin gaba daga dukkan batutuwan da suke samun kulawa daga jama'a. Me ya sa matsalar cin hanci da rashawa ke jawo hankalin jama'a sosai? Kuma mene ne shawarwarin da 'yan majalisun guda biyu suke bayar kan batun?

"Tsayawa tsayin daka kan yaki da cin hanci da rashawa, da kyautata yanayin da ake ciki game da tsare-tsare, ta yadda za a tafiyar da harkokin mulki yadda ya kamata, mataki ne da zai tabbatar da yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin jami'an gwamnatoci, da kuma harkokin siyasa."

Wannan bayani na cikin tsokacin da firaministan kasar Sin mai barin gado Wen Jiabao ya yi, yayin da yake bayar da rahoton ayyuka a madadin tsagin gwamnati.

Ayyukan da wasu jami'ai suke yi na amfani da kudin hukumomi wajen cin abinci, da amfani da motocin hukumomi, da amfani da iko don biyan bukatunsu ko dangoginsu, dukkan su laifuffukan cin hanci da rashawa ne, da ake aikatawa sakamakon rashin hanawa, da sa ido kan ikon dake hannunsu, wanda kuma hakan ke jawo nuna damuwa matuka daga bangaren jama'a.

"Za a gudanar da iko bisa tsari!". Wannan kadan ne daga bayanin da sabon shugaban jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya yi, wanda kuma ya samu martani daga bangarori daban daban a kasar ta Sin.

Dan majalisar wakilai ta jama'ar kasar Sin, Li Bin, ta ba da shawarar cewa, abin da ya fi muhimmanci wajen hana amfani da iko ta hanyar da bata dace ba shi ne, gudanar da kudaden jama'a, da albarkatun kasa, da kadarori bisa tsare-tsare da dokokin mulki suka tanada yadda ya kamata.

"Ana aiwatar da iko ta fuskar mulki ne a fannoni guda uku, wato kudin jama'a, albarkatu, da kuma kadarori, a wasu lokuta a kan samu matsaloli wajen rarraba wadannan muhimman sassa, ciki hadda yadda ake gudanarwa, da kuma sa ido kan fannonin. Saboda haka, kamata ya yi a kara sanya lura kan ikon gudanar da harkoki a wadannan fannonin guda uku yayin da ake kokarin canja nauyin dake kan gwamnati, da kyautata tsare-tsare."

Dan majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, Gong Fuwen, wanda ke yin nazari kan dokoki cikin dogon lokaci yana ganin cewa, ana bukatar karfafa dokoki ta fuskokin yin rigakafi, da yanke hukunci, da kuma sa ido kan cin hanci da rashawa.

"Game da kafa dokoki na yin rigakafin cin hanci, ban da dokokin ma'aikatan gwamnati, da na tafiyar da harkoki, kamata ya yi kuma, a ci gaba da kafa dokoki dangane da tsare-tsaren gudanar da hukuma, da na dokokin zartas da manufofin hukumar da sauransu.

Game da yanke hukunci kan cin hanci da rashawa ma, kamata ya yi a kara kaddamar da dokokin yaki da cin hanci da rashawa, da na yaki da barnata dukiyoyi, da sauransu. Ta fuskar sa ido kuma, za a kaddamar da dokokin sa ido, da kuma tsara dokokin ba da labari, da na kai kara, da kuma watsa labaru."

Kamar yadda Gong Fuwen yace, 'yan majalisun biyu dake mayar da hankali kan kafa dokoki, game da yaki da cin hanci da rashawa suna da yawa, kuma shawarwarin da suka bayar a fannin sun riga sun samu karbuwa. Mataimakin daraktan kwamitin kula da harkokin dokoki na kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Lang Sheng, ya yi bayani a kwanan baya cewa, a shekaru biyar masu zuwa, majalisar za ta kara kyautata dokoki game da yaki da cin hanci da rashawa, domin kafa wani tsarin da ya dace, wajen yanke hukunci da yin rigakafin da cin hanci da rashawa. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China