in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron shekara-shekara na majalisar CPPCC
2013-03-03 20:24:40 cri






 

Da yammacin yau Lahadi 3 ga watan da muke ciki ne aka bude taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC a nan birnin Beijing. Wannan kuma shi ne taron shekara-shekara na farko da 'yan majalisar ta CPPCC karo na 12 suka halarta, a cikin wa'adin aikinsu na shekaru biyar masu zuwa. A cikin kwanaki 9 masu zuwa, ake sa ran 'yan majalisar fiye da 2200 za su zabi shugaban sabuwar majalisar ta CPPCC da mataimakinsa, kana za su tattauna da kuma bayar da shawarwari kan muhimman manufofin kasar Sin da suka shafi siyasa, da tattalin arziki, da zamantakewar al'umma da dai sauransu.

Majalisar CPPCC dai na aikin ba da shawarwarin koli ne, don gane da harkokin siyasar kasar ta Sin, kuma muhimmiyar hanya ce ta yin shawararin demokuradiyya a kasar. A zaman taron shekara-shekara na majalisar, ba da shawara ga hukumomin tsara manufafi wani aiki ne na 'yan majalisar.

A bana, Wang Aijian, wata yar majalisar ta halarci taron ne tare da wata shawara kan raya tattalin arziki na dogaro da kai.

"Bunkasar tattalin arziki na dogaro da kai na da muhimmanci kwarai da gaske a wannan lokaci na sauye-sauye a Sin. Abkuwar matsalar hada-hadar kudi ta duniya, ta jawo koma baya kadan ga bunkasuwar tattalin arziki na dogaro da kai ga jama'ar kasarmu.

Kamata ya yi a kara raya wannan fanni a nan gaba, domin kasancewarsa jigon bada gudummawa mai yawa wajen samar da guraben aikin yi. Mutane kimanin kashi 80 cikin dari sun samu aikin yi a kamfanoni masu zaman kansu."

A wannan rana ta 3 ga wata, Wang Aijian tana cikin wadanda suka halarci babban dakin taruwar jama'a, domin halartar bude taron shekara shekara na majalisar CPPCC, inda shi da sauran 'yan majalisar fiye da 2200, suka saurari rahoton aiki da Jia Qinglin, shugaban majalisar karo na 11 ya gabatar, a madadin mambobin zaunannen kwamiti na majalisar CPPCC karon da ya gabata.

A cikin rahoton, Jia ya furta cewa, a cikin shekaru biyar da suka gabata, ayyukan gyare-gyare da raya kasar Sin, sun gamu da wahalhalu masu tsanani, wanda tinkarar kalubale, da matsalar kudi ta duniya ke cikin su. Game da wannan batun, 'yan majalisar sun bayar da shawarwarinsu cikin yakini, duka dai domin bayar da gudummawa wajen inganta ci gaban tattalin arzikin kasar Sin yadda ya kamata. Jia ya kara da cewa,

"A cikin shekaru 5 da suka gabata, muna tsayawa tsayin daka kan dora muhimmanci ga neman samun bunkasuwa bisa kimiyya da fasaha, kuma mun dauki raya tattalin arziki a matsayin ginshiki, tare da mai da hankali sosai kan bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma bisa manyan tsare-tsare a dukkanin fannoni. An gudanar da taron musamman kan harkokin siyasa da sauran batutuwa har sau 11, an kuma gudanar da ayyukan nazari 509, tare da fitar da shawarwari masu ma'ana dake da tarin yawa."

Ban da wannan kuma, a cikin wadannan shekaru biyar da suka wuce, ko da yaushe majalisar CPPCC na maida hankali ga batun gabatar da shawarwarin da suka shafi raya sabbin sana'o'i, da bunkasa birane da yankunan karkara, kana da na tafiyar da tsare-tsaren teku, wadanda aka shigar da su cikin shiri na 12 na bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin, wato wanda za a aiwatar daga shekara ta 2011 zuwa ta 2015.

Bugu da kari Jia ya ce, majalisar ta yi bincike kan batutuwan da jama'a suka fi lura da su, wadanda ke da nasaba da muradunsu, sa'an nan ta gabatar da shawarwari a fannonin sa kaimi ga samun ilmi cikin adalci, da kyautata aikin samar da guraban aikin yi na birane da yankunan karkara, da bunkasa sabon salon inshorar tsoffi a yankunan karkara da dai sauransu, wanda hakan ya kara bunkasa kyautatuwar zaman rayuwar al'ummar kasar ta Sin.

Yayin da yake bayani kan fasahar da aka samu dama ababen lura, Jia ya jaddada cewa, ko da yaushe ya kamata majalisar CPPCC ta mai da hankali sosai kan muradun jama'a. Yana mai cewa,

"Kamata ya yi mu dora muhimmanci kan moriyar jama'a, mu yi la'akari da cewa, mene ne jama'a ke bukatar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin ta yi, mene ne majalisar ke iya yi, da kuma mene ne ta riga ta yi domin jama'a. Kamata ya yi a samu fahimta daga wajen jama'a, tare da samun hidimomi daga wajensu, a kokarin kyautata ingancin shawarwarinsu yadda ya kamata."

A cikin wadannan 'yan majalisa na CPPCC, akwai wakilai 1080, dake halartar majalissar a karo na farko, wato sabbi, da kuma tsoffi wadanda suka zo birnin Beijing tare da shawararinsu kan ci gaban kasa, da kuma wadanda suke da nasaba da muradun jama'a.

A cikin kwanaki 9 masu zuwa, ake sa ran za su zabi sabbin shugabannin majalisar, kana za su tattauna, su kuma bayar da shawarwari kan muhimman manufofin kasar Sin da suka shafi siyasa, da tattalin arziki, da zamantakewar al'umma. Kawo yanzu dai, taron ya riga ya samu shawarwari fiye da 1000, wadanda suka shafi kiyaye muhallin halittu, samun ilmin cikin adalci da dai sauransu. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China