in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habaka bukatun cikin gida da kara zuba jari za su ci gaba da zama muhimman bangarori biyu dangane da raya tattalin arzikin kasar Sin
2013-03-06 18:06:49 cri






Direktan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Zhang Ping, ya bayyana cewa a yau Laraba 6 ga wata a nan birnin Beijing, habaka bukatun cikin gida, da kara zuba jari za su ci gaba da zama muhimman bangarori biyu, da za a baiwa muhimmanci wajen raya tattalin arzikin kasar Sin. Kuma yana da imani ganin bunkasuwar tattalin arzikin kasar ta Sin yadda ya kamata nan gaba.

A gun taron manema labaru da cibiyar yada labarai ta taro na farko, na majalisar wakilai na 12 na jama'ar kasar Sin na wannan rana, Zhang Ping wanda ya halarci irin wannan taro har sau biyar, ya amsa tambayoyi da manema labaru suka gabatar masa, dangane da wasu manyan batutuwan dake jan hankalin jama'a, ciki hadda hanyar da Sin za ta bi wajen raya tattalin arziki, da manufar habaka bukatun cikin gida, da raya birane da kauyuka da sauransu.

A cewarsa Sin ta fuskanci koma bayan tattalin arziki sakamakon kalubaloli daga gida da waje a shekarar bara. Kasashen duniya na mai da hankali sossai kan saurin bunkasuwar tattalin arzikinta, don gane da yadda Sin ta kasance kasa da ta kai matsayi na biyu a fannin karfin tattalin arziki a duniya. A gun taron manema labaru, Zhang Ping ya darajanta ci gaba da Sin ta samu ta fuskar tattalin arziki. Ya ce:

"Sin ta samu bunkasuwar tattalin arziki har kashi 7.8 cikin dari a shekarar bara, wanda ya ragu da kashi 1.5 cikin dari idan an kwatanta shi da na shekarar 2011, yayin da adadin yake kashi 9.3 bisa dari. Duk da haka, ya kamata, mu jinjinawa nasarar da aka samu bisa dalilai hudu. Na farko, bunkasuwa da Sin ta samu ya karu fiye da yadda aka yi tsamani a da na kashi 7.5 bisa dari. Na biyu kuwa, Sin ta samu wannan ci gaba ne karkashin matsalar hada-hadar kudi da dukkanin duniya ke fuskanta. Sannan kuma, Sin ta samu ingantuwar bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri. Sa'annan a karshe, saurin karuwar tattalin arzikin Sin ya dace da halin da muke ciki yanzu, wato shekaru 30 bayan ta dauki matakin yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje."

A halin yanzu, duniya na fuskantar koma bayan tattalin arziki, a matsayin wata kasa da ta dauki babban nauyin dake bisa kanta na ciyar da tattalin arzikin duniya gaba. An nuna kyakkyawan fata ga makomar tattalin arzikin kasar ta Sin.

Haka nan Zhang Ping, yana da imani ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin nan gaba. Inda ya ce:

"Muna iya yin amfani da zarafi mai kyau, har wa yau kuma muna da hasashen samar da kayayyaki masu inganci, bayan daukar matakan yin kwaswarima da bude kofa ga kasashen waje, tsahon shekaru 30 da Sin ta gudanar. Ban da haka, Sin na kokarin tabbatar da bunkasuwar masana'antu, da sadarwa, da raya birane da kauyuka, da bunkasa sha'anin noma bisa fasahar zamani, matakan da suka samar da bukata a gida matuka. Za a ci gaba da habaka bukatu a cikin gida, ta yadda za a bunkasa tattalin arzikin kasar cikin dogon lokaci."

Idan za a iya tunawa, Sin ta kan dogaro da cinikayyar shige da fice ne, da zuba jari, da habaka bukatun cikin gida a cikin shekarun nan da suka gabata. Amma, a baya-bayan nan an fuskanci mawuyacin hali ta fuskar cinikayyar shige da fice musamman ma a shekarar bara. Saboda haka, aka dauki matakin habaka bukatun cikin gida, tare da cimma nasara mai armashi. Yayin da yake amsa tambaya da aka gabatar masa dangane da wannan batu, ya ce:

"Ya kamata a ci gaba da samun bunkasuwar tattalin arziki ta hanyar habaka bukatun cikin gida bisa matakai uku. Na farko akwai kara kudin shiga na jama'a, ta yadda za a dada karfinsu na sayen kayayyaki. Na biyu kuwa, a tabbatar da farashin kayayyaki da habaka bukatun jama'a. Sannan kuma a kyautata halin da ake ciki a wannan fanni, wato tabbatar da ingancin kayayyaki, da kara sa ido kan kasuwa."

Dadin dadawa, Zhang Ping ya ce, ya kamata, a mai da hankali kan kyautata zaman rayuwar jama'a nan gaba, da kuma ci gaba da raya kauyuka, wadatar da manoma da kuma sa kaimi ga bunkasuwar sha'anin noma, tare da gina manyan kayayyakin more rayuwa, da kuma kara zuba jari kan sha'anin kiyaye muhalli da yin tsimin makamashi.

A halin yanzu, an mai da hankali sosai kan raya birane da kauyuka gaba daya, game da wannan batu, Zhang Ping ya fayyace cewa, kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na yi hadin gwiwa da hukumomin da abin ya shafa, domin samar da shirin raya birane da kauyuka gaba daya, wanda ake fatan gabatar da shi a rabin farkon wannan shekara. Matakin da zai taimaka wajen gudanar da wannan aiki yadda ya kamata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China