Ta kara da cewa, a jiya Litinin 10 ga wata, an yi jigilar makamai masu guba karo na uku, kuma ana shirin kai su zuwa kasashen waje. Bisa shirin da kasashe daban-daban suka tsara na ba da kariya ga wadannan jiragen ruwa, jirgin ruwan yaki na kasar Sin Yancheng ya kammala wannan shirin hada kai da sauran jiragen ruwan yaki ciki hadda na kasar Rasha. Ya zuwa yanzu, jirgin ruwan yaki na Yancheng zai jira umurni na gaba. Hua Chunying ta kara da cewa, Sin na maraba da kokarin da bangarori daban-daban suka yi, don tabbatar da shirin kawar da makamai masu guba, tare kuma da fatan kara yin mu'ammala da bangarori daban-daban ta yadda za su hada kai domin tabbatar da lafiyar jiragen ruwan da ke sufurin makamai masu guba na kasar Sham. (Amina)